✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyanwa ta samu gadon sama da Naira biliyan 72

Kyanwar wani fitaccen tela dan kasar Jamus marigayi Karl Lagerfeld, mai suna Choupette, za ta gaji tsabar kudi da ya kai Dalar Amurka miliyan 200…

Kyanwar wani fitaccen tela dan kasar Jamus marigayi Karl Lagerfeld, mai suna Choupette, za ta gaji tsabar kudi da ya kai Dalar Amurka miliyan 200 (kimanin Naira biliyan 72 da miliyan 192). bayan da telan ya yi wasiyyar cewa  kyanwar ce za ta gaje shi idan ya rasu.

A cewar rahoton gidan rediyon BBC, kwararren telan wanda ya rasu yana da shekara 85, kafin ya rasu ya bar wasiyyar cewa, kyanwarsa ita ce za ta gaji kudin da ya bari.

Marigayi Karl Lagerfeld ya fada wa Mujallar Faransa Numero a bara cewa, ya rubuta sunan kyanwarsa a matsayin wadda za ta gaji rukunin gidajensa bayan rasuwarsa.

Kyanwar dai ta kasance dabba mai dukiya, kuma rahotanni sun bayyana cewa an yi amfani da kudin shigar kyanwar da suka kai Dalar Amurka miliyan uku, wajen tallata kamfanin motocin Jamus da wasu kayan kamfanin man kwalliya duk da tambarin marigayin Lagerfeld.

Kafin rasuwar marigayi Karl Lagerfeld, a tattaunawa daban-daban da ya yi da majiyar Mujallar Numero, ya dauki ’yan aikin gida biyu na musamman da za su rika lura da kyanwar sannan a koyaushe ana shirya wa kyanwar kayan abinci nau’i hudu a cikin kwanukan abinci na alfarma.

Ya dai bude wa kyanwa Choupette shafuffukan sadarwar zamani na Tiwita da Instagram kuma wannan shafin na kyanwar yana da mabiya da suka kai dubu 200 masu bibiyan shafin a koyaushe.

Masu bin shafin su yi ta tura sakon ta’aziyyar rasuwar marigayi Karl Lagerfeld a shafin Tiwita na @ChoupettesDiary.

Wasu sakonni na bayyana cewa, ba za su manta da ayyukan marigayi Karl Lagerfeld ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya bayyana cewa, marigayi Karl Lagerfeld ya rasu yana da shekara 85 a birnin Paris na kasar Faransa.

Karl Lagerfeld ya yi fice a fannin kirkirar dinkin sutura wanda yake da mukamin Darakta tun daga 1983 har zuwa lokacin da ya rasu. Ya kasance gwani a fannin nau’in dinkuna a duniya.

A yayin da jama’a ke nuna alhinin rashin marigayi Karl Lagerfeld wasu kuma hankalinsu ya koma ne kan kyanwarsa Choupette da take dabba mai arziki a kamfanonin dinka sutura.