Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
La-Liga: Gobe za a yi Karon-Battar Madrid - Aminiya
Aminiya

La-Liga: Gobe za a yi Karon-Battar Madrid

A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a gwabza a tsakanin kulob din Atletico Madrid da na Real Madrid a gasar La-Liga ta Spain a wasan da ake kira da Karon- Battar Madrid.

Za a yi wasan ne a filin wasa na Atletico Madrid da misalin karfe 8:00 na dare agogon Najeriya.

Kawo yanzu kulob din Real Madrid ne yake sama a teburin gasar da maki 14 yayin da Atletico Madrid ke matsayi na 2.

Sai dai kafin nan, kulob din Getafe zai kara da kulob din FC Barcelona da misalin karfe 3:00 na rana yayin da Atletico Bilbao zai hadu da Balencia da misalin karfe 12:00 na rana.  Sai  Granada da Leganes za su kece raini da misalin karfe 5:30 na yamma a agogon Najeriya.

ADVERTISEMENT