✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

La-Liga:  Jibi za a gwabza tsakanin Sebilla da Real Madrid

A ci gaba da fafatawa a gasar La-Liga ta Spain, a jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a gwabza a tsakanin kulob din Sebilla…

A ci gaba da fafatawa a gasar La-Liga ta Spain, a jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a gwabza a tsakanin kulob din Sebilla da Real Madrid.

Kawo yanzu kulob din Sebilla ne yake saman teburin gasar bayan ya hada maki 10 a wasanni 4 yayin da kulob din Madrid yake matsayi na uku da maki 8 a wasanni hudu.

Kulob din Atletico Madrid ne na biyu da maki 10 sai kulob din Atletico Bilbao a matsayi na 4 da maki 8.

Kulob din FC Barcelona yana matsayi na 5 ne da maki 7 a wasanni hudu.

Sai dai a gobe Asabar ce kulob din Atletico Madrid zai kara da Celta Bigo da misalin karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya yayin da Granada zai  hadu da Barcelona da misalin karfe 8:00 na dare agogon Najeriya.