✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Agogon Manomi

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Ina fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo maku ‘Labarin Agogon Manomi’ ne. Wannan labarin yana koya wa…

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Ina fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo maku ‘Labarin Agogon Manomi’ ne. Wannan labarin yana koya wa Manyan Gobe yadda za su zama masu natsuwa a koyaushe don cimma burinsu. A sha karatu lafiya.

Taku:  Amina Abdullahi

Akwai wani manomi ne yana da agogo mai matukar kyau. Wata rana yana cikin aiki a cikin rumbunsa, sai ya nemi agogo ya rasa inda ya saka shi. Sai ya shiga neman agogon a rumbunsa. Ya duba duk inda yake tsammanin ganin agogon amma bai gani ba.

Sai ya yanke shawarar fada wa yaran da ke wasa kusa da gonarsa. Ya ce su taimake shi su nema masa agogon kuma yana da wata babbar kyauta ga wanda ya ga agogon.

Yara suka shiga rumbu neman agogo don samun kyauta daga manomi. Bayan sun yi minti 30, sai suka fito daga rumbu ba wanda ya samu agogo. Sai manomi ya hakura. Yana faman rufe rumbunsa, sai wani yaro daga cikin yaran ya ce da shi, a ba shi damar sake shiga rumbun kila ya yi nasara.

Sai manomi ya ba shi dama. Bayan wasu mintuna, sai yaron ya fito da agogo. Manomi ya yi mamakin yadda yaron ya samu agogon bayan ’yan uwansa sun shiga ba su gani ba. Sai ya tambayi yaro yaya aka yi ya ga agogon? Sai yaro ya ce, da ya shiga rumbun, ya zauna shiru ne kuma ya natsu can sai ya fara jin sautin agogo. A haka ya rika bin sautin har ya samo agogon.

Manomi ya cika wa yaron alkawarin kyautar da ya yi niyyar bayarwa.

Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labari. Ko me za a yi yana da kyau mutum ya samu natsuwa don cimma burinsa.