Da Dumi Dumi

Labarin amarya mayya (2)

Maigida bai yarda da wannan magana ta Malam ba don haka ya tashi ya fice daga wurin.

Bayan an dauki tsawon lokaci ba a daina yi wa dabbobinsa dauki daidai ba don haka maigidan ya sake komawa wajen Malam a karo ana biyu.

Malam ya sake tabbatar masa cewa amaryarsa ce mayya take cinye masa dabbobi. A nan ne maigidan ya tambayi Malam abin da za a yi don yin maganin matsalar. Sai Malam ya ce idan ka je gidan ka gaya wa matarka za ka yi tafiya. Sannan idan gari ya waye sai ka koma gidan ka samu wuri ka boye za ka ga abin da zai faru a kan idonka. Maigida ya kawo kudi ya ba Malam shi kuma ya karba yana  godya.

Mu kwana nan.

ADVERTISEMENT
Share