Aminiya

Labarin Amarya Mayya (3)

Lokacin da maigida ya isa gida sai ya tara matansa kamar yadda ya saba ya sanar musu cewa gobe zai yi wata tafiyar, jin haka ya sa amarya yin murna ita kuwa uwargida sai ta fara tambayarsa dalilin komawarsa a kankanen lokaci inda shi kuma ya amsa mata cewa jama’ar yankin ne ke bukatar dabbobi. Daga nan ya yi   sallama da su sannan ya tafi.

Kafin dare ya yi sai maigidan ya yi wata shiga ya bad da kama sannan ya koma gidansa ya buya. Da dare ya yi sai amarya ta fito ta kama dabba daya ta kwada da kasa ta yagi cinya ta cinye sannan ta koma dakinta kamar babu abin da ya faru. Shi kuwa maigida wanda ke labe a lokacin da da take gudanar da wannan lamari ya shiga dakin uwargidan sai ta fara mamakin ganinsa.   A nan ya gaya mata cewa ba su samu mota  ba ne don haka ya fasa tafiyar. Daga nan  ya ce ta kira masa amarya.  Tana shigowa ta bude baki alamar mamakin ganinsa ba ta rufe baki ba maigidan ya sanar da ita duk abin da ya gani. Nan take ya sake ta.

Darasin labarin:

Yana nuna mana muhimmancin yin bincike kafin a yi aure. Yana da kyau mutane su rika yin bincike don sanin wa za su aura tare da guje wa daukar kara da kiyashi.

 

ADVERTISEMENT