✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Labarun karya ne suka haifar da rikici a Legas’

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana labarun kanzon-kurege da ake yadawa a kafofin sada zumunta akan zanga-zangar #EndSARS da cewa sune suka jawo tashin…

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana labarun kanzon-kurege da ake yadawa a kafofin sada zumunta akan zanga-zangar #EndSARS da cewa sune suka jawo tashin hankali a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin tattaunarwasa da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis.

Sanwo-Olu ya kara da cewa tasirin labarun karya da ake yadawa ne ya janyo bata gari fasa shagunan mutane, da farfasa kayan gwamnati tare da kai farmaki kan mutanen da ba ruwansu.

Gwamnan ya ce, “Kafofin sada zumunta na zamani suna da matukar amfani da tasiri a wannan zamani, amma idan bamu yi amfani dasu ta hanyar da suka dace ba zamu iya jefa rayuwar mutane da dama cikin hadari”.

“Ya kamata a ce muna tantance irin bayanan da muke wallafawa a kafofin sada zumuntar da muke amfani dasu”, cewar Sanwo-Olu.

Sakamakon rikicin da ya barke a jihar Legas, gwamnan ya ce ya gayyaci masu ruwa da tsaki na jihar, wanda suka hada da shugabannin addinin Musulunci dana Kirista, domin samar da mafita daga halin da jihar ta tsinci kanta a ciki.

Gwamnan ya ja hankalin mutanen jihar dasu hada kai wajen samar da mafita da kuma dauwamamen zaman lafiya.

Daga karshe yace akwai yuwuwar a sassauta dokar kullen da aka saka a  jihar a ranar Juma’a ko Asabar, domin ba wa mutane damar zuwa neman abinci.