Aminiya

Ladubban neman aure (5)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladabi na biyar, shi ne zaben macen da ta dace. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Abubuwan dubawa wajen nazarin rikon addinin macen da ake neman aurenta; ci gaba…

ADVERTISEMENT

3. Mace mara tarbiyya na iya rikidewa ta zama nagartacciyar mace mai tarbiyya bayan aure. Wannan na iya faruwa ne kadai in macen ta kasance mai kyakkyawar zuciya, ta kasance mara tarbiyya ne kadai don ba ta samu tarbiyyar ba a gidansu, amma in ta samu tarbiyya a gidan miji sai wannan ya sa ta zama nagartacciya. Domin akan samu wadansu mata marasa kamun kai, amma aure ya sanya su natsu su kama kansu.

4. Kasancewar mace ta fito daga babban gida, ba shi ke nuna tana da tarbiyya ko riko da addini ba, ba kuma shi ke nuna za ta zamo nagartacciyar matar aure ba. Sai dai maniyyacin aure ya auna ya yi nazari ta kowace fuska, ya yi aiki da umarnin Annabi (SAW) na cewa a nemi mace mai riko da addini, in har ta cika dukkan sharuddan riko da addini, kasancewar ta ’yar babban gida sai ya zama karin ni’ima ke nan, in kuma ba ta cika sharuddan ba, to kasantuwarta ’yar babban gida ba zai yi kyakkyawan tasiri ba.

ADVERTISEMENT

5. Yawan ilimin addini ba shi ke nuna cewa mace mai rikon addini ce ba, da yawa akwai mata masu ilimin addini amma kuma ba sa aiki da iliminsu. Wadansu ilimin nasu ma shi ke sa su zama masu takama da jiji-da-kai wanda hakan ke kai su ga aikata kura-kurai da yawa wadanda suka ci karo da siffar riko da addini.

6. Kamun kai, natsuwa da yawan jin kunya ba shi ke tabbatar da mace mai riko da addini ba ce,  domin akan samu mata masu irin wannan siffar, amma can a boye suna aikata wata tabargazar da ta ci karo da siffar riko da addini.

Hanya mafi sauki ta gane yanayin zamantakewar macen da ake nema da aure shi ne ta hanyar yin bincike da nazarin zamantakewar mahaifiyarta a gidan mahaifinta, ko kuma duk wata macen da ta tashi ta girma a gabanta. Matan da ta girma a cikinsu, irin yadda suka yi zaman aurensu, ita ma haka za ta yi, sai dai ikon Allah ne kadai ke iya sawa a samu akasin haka. Wannan saboda la’akari da cewa kowane yaro yana dubi ne ga al’adar gidansu ya koyi yadda zai yi tasa rayuwar. Kamar yadda Hausawa kan ce: ‘Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi,’ kuma masana kimiyyar zamantakewa sun tabbatar da hakan: cewa  akasarin mutane, yadda iyayensu suka yi rayuwar aure, to haka su ma za su yi.

2. Zabar masoyiyar mace: Bayan an tabbatar macen da ake da niyyar aure tana da rikon addini, daga nan sai a yi binciken ko ta iya zamantakewar soyayya ta aure? Annabi (SAW) ya yi umarni ga al’ummarsa cewa:

“Ku auri masoya kuma masu haihuwa (daga mata), don in yi alfahari da yawanku a Ranar Kiyama.

Haka kuma Annabi (SAW) ya ce:

“Ku auri ’yan mata, domin bakinsu ya fi zaki, kuma mahaifarsu ta fi saurin daukar ciki sannan suna hakuri da kadan.”

Haka kuma ya ce da sahabinsa Jabir dan Abdullah (Allah Ya kara yarda a gare shi):

“Me ya sa ba ka auri budurwa ba, ka yi mata wasa, ita ma ta yi maka?”

In muka yi nazarin wadannan maganganu na Manzon Allah (SAW), za mu fahimci suna nuna muhimmancin zaben macen da ta iya zamantakewa mai kyau, wadda ta iya soyayya irin ta aure kuma ta kasance mai amsar soyayyar mijinta; wadda in mutum ya aure ta, zai ji dadin zama da ita, zai yi wasa da ita, ita ma za ta yi wasa da shi, wadda za su rika rige-rigen faranta wa juna rai shi da ita. Sannan budurwar mace zuciyarta fes take, daudar dawainiyar yau da kullum na rayuwa ba su fara yin tasiri a zuciyarta ba, don haka zuciyarta cike take da kyawawan tunani da abubuwan kayatarwa da faranta rai da kuma karancin munanan tunani ko abubuwan munana rayuwa. In aka samu fasihin magidanci sai ya ci gaba da tarbiyyarta a kan haka sai ya mori wannan kyakkyawar dabi’a har zuwa tsufa.

Sai mako na gaba insha Allah.  Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.