✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban zabar mijin aure (5)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fata Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za…

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fata Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladubban da mace Musulma za ta yi amfani da su wajen zabar mijin aure, inda za mu karasa bayani kan ladubban lokacin jiran fitowar miji mafi dacewa. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin:

Ladubban ’yan matanci…Ci gaba

Ladubban hira da samari: Da farko dai mu sani, bai daga cikin koyarwar addinin Musulunci yin hira da samari a kofar gida ko a cikin zaure ko a cikin gida ko a cikin mota. Wannan yana daya daga cikin al’adun Malam Bahaushe da suka ci karo da addini. Bayan haka kadaituwar saurayi da budurwa ana hira ko a wane irin muhalli ne, matukar su biyu ne kadai ba wani a tare da su, wannan haramtaccen zama ne, kuma shaidan shi ne na ukunsu a irin wannan zaman kamar yadda ya zo a ingantaccen Hadisin Manzon Allah (SAW). Don haka irin wannan hira, ko da da saurayi daya ne wanda aka tsayar da magana da shi, haramun ne, balle kuma da samari daban-daban ta yadda a wani wajen ma har layi suke yi wajen hira da budurwa daya.

Duk da cewa ana fakewa da cewa amfanin wannan hira shi ne don gina fahimtar juna a tsakanin maniyyata auren biyu; bincike ya tabbatar fahimtar juna da aka gina kafin aure ba ta da wani tasiri na a-zo-a-gani bayan aure! Dalilin haka kuwa shi ne domin lokacin da ake irin wannan hira, dukkan saurayi da budurwar suna cikin kawa-zucin juna, kowa bai da buri sai na yadda zai burge dan uwansa, don haka ba wanda zai fito da ainihin gundarin halinsa ya bayyanar ga dan uwansa; kuma ko da ya so ya bayyanar din ma, to ba zai bayyanu ba a asalin yadda halayyar mutum take. Saboda ba a zaune tare da juna a kowane lokaci; kuma ba a zaune a muhalli daya, sai dai a yi hira na wani takaitaccen lokaci a rabu. Yin wannan hira bai isa ga gina ingantacciyar fahimtar juna ba; wannan ya sa ainihin gundarin hali da dabi’a suna bayyanuwa ne kadai bayan an yi aure, an zauna tare a muhalli daya kuma an yi hulda da juna ta hanyoyi daban-daban. Hakan kuwa na faruwa ne domin shi aure irin kalubalensa daban da na rayuwar samartaka. Bayanin ladubban ingantacciyar hira da ta dace da koyarwar addinin Musulunci ya riga ya gabata a wannan fili; ga ladubban da dukkan mace Musulma ya kamata ta kiyaye wajen hira da maneman aurenta:

Kiyaye kadaituwa lokacin hira: Kamar yadda ya gabata a bayanin da ke sama, haramun ne kadaituwar mace da namijin da ba muharraman juna ba; don haka ’yar uwa ki kiyaye wannan, don yin haka ya zama ruwan dare a cikin al’umma, kuma ya zama al’ada ba shi ke nuna cewa abin nan yana da wata fa’ida ba;  ba kuma shi zai sa ya zama dole ke ma sai kin aikata shi ba. Ki tuna, ke kadai Allah Zai yi wa hisabi, kuma babu mai taimakonki daga cikin iyaye da kawaye ko samarinki, lokacin da Allah Zai tambaye ki game da iyakokin da Ya aza miki na addini. Don haka ki yi biyayya ga dokokin Allah don samun dacewa a duniya da lahira.

Yin hira da samari sama da daya: Wannan ma ba daidai ba ne kuma bai dace da duk wata mace mai kunya mai mutunci ba, a ce ta tara samari sama da daya, kowanne ya zo ya zuki dadin hirarki ya ba ki tukuici ya tafi; har irin haka ya zama wani abin burgewa a ce a cikin al’umma, a rika cewa ‘ai wance tana da farin jini, samari har layi suke a kofar gidansu,’ da sauran ire-iren wadannan kalamai. Duk namijin da kika tabbatar ba aurensa za ki yi ba, to ba dalilin ki tsaya kina hirar bata lokaci da shi.

Rashin sanya cikakken hijabi: Haramun ne ga ’ya mace ta bayyana ga mazan da ba muharramanta ba sai tare da cikakken hijabi kamar yadda ayoyin Alkur’ani Mai girma suka bayyana. Don haka yin hira cikin kaya masu bayyanar da kirar ’ya mace haramun ne kuma bai dace da dukkan wata mace Musulma ba.

Caba ado: Haka kuma ba ya daga cikin koyarwar addinin Musulunci caba ado lokacin yin hira da samari dukkan ado na fuska da na jiki; haka na sanya turare mai zafin kanshi da har wani zai iya jiyo shi, shi ma haramun ne.

Amsar kudin hira: Yin hira ba da niyyar aure ba sai don niyyar kawai a ci kudin haram ne kuma bai dace da duk Musulma mai kyakykyawar tarbiyya ba.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.