Aminiya

Ladubban zaben mijin aure

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan ladubban da mace Musulma za ta yi amfani da su wajen zaben mijin aure. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Ladubban jiran fitowar miji mafi dacewa:

ADVERTISEMENT

Ladabi na 1: Kyakykyawan Kudiri: Kulla niyyar lokacin yin aure ga ’ya mace ya fi ta’allaka ne ga iyayenta, domin su za su kulla niyyar su aurar da ita a lokaci mafi dacewa gare su. Ko a lokacin bayyanar miji mafi dacewa ga ’yarsu. Duk da haka yana da kyau ga wadda ta mallaki hankalin kanta ta kulla kyakkyawar niyya a zuciyarta game da aure, domin aure ibada ce gare ta kamar yadda yake ibada ga namiji. Don haka sai mace Musulma ta kulla niyyar ayyukan alheri da suka dangaci aure kamar bin ka’dojin addini dukkansu yayin da take zaman jiran fitowar miji mafi dacewa gare ta, kamun kai, hakuri, yin ladabi ga iyaye da magabata, kudirin yin zaman aure domin Allah da fatar samun kyakkyawan sakamako, da sauran kyawawan kudirori da suka dace da yanayi da kuma lokaci.

Ladabi na Biyu: Tsananta Addu’a:

ADVERTISEMENT

Sai mace Musulma ta dage a halin jiran fitowar mijin aure ta kasance mai tsananta addu’a da kara dagewa wajen tsayar da addininta da yin abubuwan karuwar imani a zuciya, kamar yawan yin azumin nafila a-kai-a- kai, sallolin nafila a sulusin karshe na dare, yawan yin sadaka, karin kyautatawa ga iyaye, ’yan uwa makusanta da makwabta. Yawan yin Sallar neman zabin Allah (Sallar Istikhara); dagewa wajen guje wa aikata ayyukan sabon Allah, musamman  kanana irin wadanda aka raina; guje wa cin haram; yawan yin tasbihi da istigifari da raya zuciya da yawan tuna Allah Madaukakin Sarki da yawan gode maSa.

Ladabi na Uku: Biyayya ga dokokin Allah:

Wajibi ne ga mace Musulma, ta kiyaye dokokin addini gaba dayansu lokacin da take zaman jiran fitowar mafi dacewar miji gare ta. Wannan kuwa shi ne kasancewa cikin cikakken hijabi duk lokacin da za ta fita waje da kame kanta daga bayyana jiki ga mazan da ba muharramanta ba; ta san cewa bai halatta ta aikata wasu ayyukan da za su ja ra’ayin maza zuwa gare ta, kamar fita cikin shiga wacce ta saba wa addini, caba kwalliya da bayyanar da ita a koyaushe. Haka haramun ne tsayawa da samari ana hira a kofar gida ko a cikin mota. Ki sani, ya ke ’yar uwa mai karamci! Allah Ubangiji Ya sanya wasu dokoki gare ki ba don takurawa gare ki ba, a’a, sai don Ya karrama ki Ya daga darajarki kuma ya tabbatar miki da mutuncinki. Don haka ba daidai ba ne ki wulakanta kanki ta hanyar juya baya ga wadannan dokoki na Allah Madaukaki. A ce kina shiga irin shigar fajiran mata don kawai ki jawo ra’ayin maza su ce suna sonki; wannan ba shi zai jawo miki farin jini ba, ba irin abin da ke jawo farin jini ga ’ya mace kamar tsoron Allah. Ba a samun tsoron Allah kuwa sai in ana yin ladabi ga dokokinSa sau da kafa.

Ladabi na Hudu: Riko da addini: In har kina da burin samun miji mai inganci, wanda zai tsare miki dukkan hakkokinki na aure, to ki dage ki kasance mai riko da addininki komai dadi komai tsanani. Ki sani, mace mai riko da addini ita ce mafi tsadar mata a wannan zamani, domin ita ce wacce fiyayyen halitta Manzon Allah )Sallallahu Alaihi Wasallam) ya sa wa tambarin cewa ita kadai ya halatta a nema da aure. Ga shi muna cikin wani zamani da riko da addini ya zama abu mai wuyar samu a cikin al’umma. Don haka ba ki da wani abu mafi tsada kuma mafi muhimmanci gare ki a lokacin jiran miji kamar riko da addini. Kuma ki sani ya ’yar uwa mai karamci! Riko da addini ya wuce sanya zumbulelen hijabi da tara ilimin addini, tabbas wadannan dabi’u ne masu kyau kuma abin yabawa, amma riko da addini ba iyakarsa ke nan ba. Ya kunshi dagewa wajen yin ayyukan ibada da kauce wa haramtattun abubuwa da yawan yin abubuwan raya imani cikin zuciya, ta yadda da imaninki ya ragu za ki farga ki yi kokarin gyara dabi’unki na Musulunci don samun karuwar imani cikin zuciya.

Zan dakata a nan, sai mako na gaba insha Allah. Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.