Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin tambayoyi

Yarinya ce an yaye ta, har an kai ta yaye an dawo da ita amma sai dai a tashi da safe a ga ta kama mama. Ko hakan akwai wata matsala?

ADVERTISEMENT

Daga Idris Kasuwar Barci, Kaduna

Amsa: Babu wata matsala, domin a mafi yawan lokaci in dai an yaye yarinya har an kai ta wani gida tsawon wani lokaci idan ta dawo ta kama mama ba abin da zai zo. Kawai dai shaukin shan maman ne bai sake ta ba. A wasu lokutan idan aka samu irin wadannan yara da ba sa son yaye akwai wasu abubuwa da akan yi a gargajiyance wadanda ba za su cutar da ita ba, ba kuma za su cutar da uwar ba. Wani abu ake samowa mai daci a shafa a kan maman domin idan ta sha ta ji ba dadi ba za ta sake kwadayin kamawa ba. Wadansu ma kan shafa wani launi ne kawai da idan yaro ya gani ba zai yi sha’awa ba.

ADVERTISEMENT

Abin da kawai wannan ke nunawa shi ne watakila an cire ita yarinyar daga mama tun kafin ta shirya. Ana so idan za a yi yaye a tabbatar yaran sun shirya sosai. Yadda ake shiryawar kuwa shi ne ta yawan ba su abinci masu gina jiki da madarar shanu (ta gari ko ta ruwa) isassu a daidai lokutan da yayen ya karato. Wannan zai rage musu shaukin shan mama, kuma wadansu yaran da kansu za a ga sun bar shayarwar dungurungum.

 

Ko akwai wata illa da za ta iya samun yaron da ba a cire wa ’yar wuya ba?

Daga Habu Na-Habu, Deidei

Amsa: A’a ba wata matsala. A likitance ma an fi son hakan, kada a cire din a bari a ga yadda aikinta zai kasance, wasunsu sukan yi aikin da ya kamace su, wasunsu kuma sai an cire. Domin da ma su ’yar wuyar ai wasu kandagarki ne ga huhu da kunnuwa, domin kada kwayoyin cuta su shige su kai-tsaye. Idan kwayoyin cuta sun shiga hanyar numfashi, su ’yar wuya su suke tare su. Shi ya sa za a ga a wasu lokutan su ’yar wuyan sun kumbura suna ciwo. Wannan alama ce ta cewa sun tare wata cuta da ta kamata ta shiga huhun ko ma kunnuwa. Kuma da an dan ba da magunguna na ’yan kwanaki za su baje, sabanin idan da an samu sun shiga huhu ko kunne.

Ai wasu al’ummu da a zamanin da suke cire wa jariransu ’yar wuya ta tiyatar gargajiya yanzu sun rage cirewa sosai. Don haka ko a al’adar Hausa ma a yanzu sai ka tona kafin ka ji gidan da aka cire wa jariri ’yar wuya. Sai dai akwai lokacin da ’yar wuya za ta damu yaro, ya kasance cewa duk bayan ’yan watanni sai ya yi ciwon wuya, wato sai ’yan wuya sun yi kumburi sun yi masa ciwo. To a irin wannan yanayi likitocin makogaro sukan ba da shawara a kai irin wadannan yara su gani ko ya dace a cire su