✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA – Amsoshin tambayoyi

Me ke kawo wa wadansu mata kuraje idan aka yi amfani da audugar mata ta pad Daga Mairo K. Amsa: Alamar audugar ba ta karbi…

Me ke kawo wa wadansu mata kuraje idan aka yi amfani da audugar mata ta pad

Daga Mairo K.

Amsa: Alamar audugar ba ta karbi jikin matar ba ke nan sai a canja da wata. Idan kuma har ila yau an canja ba a ga canji ba sai an ga likitan fata ko likitar mata.

 

Me ke kawo masu ciwon sikila samun gurgurewar kashi abin da ake kira osteonecrosis?

Daga Kwamared Habu Manja

Amsa: Ka san masu ciwon sikila jajayen kwayoyin jininsu kamar lauje (wato sickle) suke komawa maimakon kamar sisi. To idan suka zama lauje da yawa ba sa shiga sassan jiki yadda ya kamata, shi ya sa suke samun ciwon gabobi. Idan aka dade jini ba ya samu ya shiga kasusuwa shi ne ake samun gurgurewar kashi kamar yadda kake tambaya.

 

Ina da yarona dan shekara uku mai yawan jin zufa ko ruwan sama ake yi shi sai ya yi. Ko hakan matsala ce?

Daga Nuhu M. Keffi

Amsa: A’a ba matsala ba ce. Da dai kamar ka ce shi ko a lokutan hunturu ko cikin sanyin na’urar AC yana zufa shi ne za a ce akwai matsala.

 

Matata idan ta samu juna biyu wata uku na farko suna ba ta wahala daga amai sai rashin cin abinci. Sai watan hudu take samun sauki. Shin wannan matsala ce?

Daga Baban Fadila Faragai

Amsa: Eh, wannan wata matsala ce da mukan kira da suna hyperemesis grabidarum. Mace mai samun wannan matsala sai ana yi ana ba ta magunguna, idan ma ba ta iya shan magungunan to dole sai da allurai da karin ruwa. Domin idan ya yi tsanani har bari yakan jawo.

 

Wai da gaske ne abin da ake sa wa mace a hannu domin tazarar haihuwa yana kawo kansa? A mini bayani

Daga Zainab Zakari

Amsa: A’a haba Hajiya Zainab, yaya za a yi a sa mutum abin da aka san zai zame masa kansa? Ai a asibiti ba a haka. Don haka babu kanshin gaskiya a cikin zancen. Sinadarin da ake sa wa a hannu sinadarin hormone ne wanda jikin mata ke samarwa lokacin da suke da juna biyu. Yana hana sakin kwai ne. Kin ga kuwa idan ba a saki kwai ba babu juna biyu.

 

Yarinyata watanninta shida na ga canjin yanayi na je na ga likita aka auna aka ce ina da juna biyu. Zan ci gaba da shayar da ita ko kuwa madarar jarirai zan ba ta?

Daga S. Mainasara

Amsa: E, a likitance za ki ci gaba da shayarwa, ba matsala, duk da cewa a al’adance wasu za ki ji sun ba ki shawarar akasin haka.