✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA Amfanin Madigar Jarirai

Wai mene ne akan gani a kan jarirai ne yana motsi kamar bugun zuciya? Kuma mene ne amfaninsa Amsa: Madiga ce, wadda take kamar fili…

Wai mene ne akan gani a kan jarirai ne yana motsi kamar bugun zuciya? Kuma mene ne amfaninsa

Amsa: Madiga ce, wadda take kamar fili ne a kokon ka a jarirai, wato ba kashi a wurin sai fata da tsoka da magudanan jini, wadanda kake gani suna balli-balli. Wato a kan jarirai akwai kasusuwa bari biyar na kokon kai; biyu gaba, biyu gefen dama da hagu, daya kuma a baya. Tsakanin kowane kashi akwai wani gurbi a gaban kai da kuma daya a bayan kai.

Wadannan gurabe su ake kira madiga. Gurbi na gaba ya fi na baya kai girma, kuma shi aka fi sani da madiga. Wato dai ita madiga ba wata halitta bace, a’a wani gurbi ne a tsakanin kashin kan jarirai. Manufar wannan gurbi guda biyu ce; na farko shi ne idan mace ta zo haihuwa kokon kan jariri zai iya motsewa domin kai ya samu ya fito cikin sauki. Na biyu kuma shi ne domin wannan gurbi ya bar kwakwalwar jariri ta girma kafin daga baya su zo su rufe. Madigar bayan kai na rufewa ne bayan ‘yan watanni da haihuwa, amma madigar gaban kai sai yaro ya kai kimanin shekaru biyu. Wani lokaci akan iya ganin gurbi na gaba wato madiga ta gaban kai tana motsi tana bal-bal.

Wannan na faruwa ne saboda akwai magudanar jinni daidai wurin, wannan zagayawar da jini ke yi a kwakwalwa ne ke sa motsin, kuma motsin na tafiya ne da yanayin bugun zuciya, wato da zuciya sai a ga magudanan jini na madiga na amsawa. Wasu kuma sukan zaci cewa da an taba madiga an tabo kwakwalwa kenan. Har ma akan ji tsoron cewa yaron da ya dan sami buguwa a wajen kusan kwakwalwarsa ta bugu kenen. A’a ba haka zancen yake ba, domin tsakanin madigar da kwakwalwa akwai wani mayani mai kwarin gaske da yake rike da kasusuwan kokon ka ta ciki.

Wani amfani na madiga kuma shi ne cewa ana iya gane alamun rashin lafiya a jariri ta madiga. Jaririn da yake amai da zawo ko kuma wanda ya ki karbar nono haka kawai, kuma aka ga madigarshi ta fara lobawa ciki, alamu ne na cewa ya fara galabaita kenan, babu isasshen ruwa a jikinsa. Don haka a yi maza a kai shi asibiti domin karin ruwa da ba shi magani. A daya hannun kuma, jaririn da shi kuma aka ga madigarsa ta yi tauri, fatar wurin ta kumburo, to shi ma dole akai shi asibiti domin alama ce ta wasu cutuka irinsu sankarau a jarirai.