✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA … Amsoshin tambayoyi

Amsoshin tambayoyi Na yi tsarin iyali na hannuwa na biyu ke nan, an cire mini amma har yanzu ban ga alamun al’ada ba, ko lafiya?…

Amsoshin tambayoyi

Na yi tsarin iyali na hannuwa na biyu ke nan, an cire mini amma har yanzu ban ga alamun al’ada ba, ko lafiya?

Daga Saudat A.

Amsa: Eh, haka ne irin wannan na faruwa sosai kuwa, wato wadannan magunguna suna iya sa haka, duk da cewa ya kamata a ce an fada miki kafin a sa miki irin wannan magani na karkashin fatar hannuwa, saboda ki san irin hakan na iya faruwa ko don kya iya canja zabi. Amma dai babu wata matsala, wasu lokuta sai an yi wata uku ko ma fiye bayan an cire kafin al’adar ta dawo.

 

Wadanne alamomi ne ke nuna mace ko mijinta ba za su iya samun haihuwa ba?

Daga S.I.Danjanku

Amsa: A’a a likitance babu wasu alamu a fili, ko na zahiri da za a gani a hakikance ko a tabbatar cewa kawai da ganin mace a ce wannan ba za ta iya daukar juna biyu ba, ko a ga namiji a ce ba zai iya haihuwa ba. Abin a boye yake. A kimiyance sai mata ta yi aure ta zauna a gidan mijinta na akalla shekara guda ba a ga alamun juna biyu ba kafin a fara tunanin ko da matsala, a fara binciken dalili. Mijin nata kuma sai ya kasance zaunanne a gari a cikin shekarar wato ya kasance ba mai yawan tafiye-tafiye ba. a kimiyance kashi 40 cikin 100 na matsalar rashin haihuwa daga matar ce, wasu kashi 40 daga mijin, sauran kashi 10 ne sukan raba a tsakaninsu.

 

A wasu lokuta nakan ga yarona yana zufa da gumi a hammata duk da bai fi shekara 10 ba. Ko hakan na nufin ya fara girma?

Daga Maman Khalid

Amsa: Eh, duk da cewa wasu yaran komai kankantarsu idan suka shiga rana suka yi wasa sukan yi gumi da tsami wanda akan kira da warin rana, amma hakan ya fi faruwa ga yaran da suka haura shekara 10 da haihuwa, tunda wadannan shekaru su ne na farko-farkon girman yara daga kanana zuwa manyanta.Wato daga shekara 10 da haihuwa za a iya fara ganin alamun girma a yara ta hanyar tsamin jiki da gumin hammata da sauransu. A irin wannan lokaci za a rika yawan karfafa musu gwiwa wajen yawan tsabtar jiki, kamar wanka kullum da ma wanka kamar sau biyu lokutan zafi, ko a lokutan da aka je aka yi wasanni aka yi zufa, har ma da shafa irin abin da manya kan shafa da kan hana zufar hammata, kamar su hoda da man hammata na roll-on da sauransu.