Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

LAFIYAR MATA DA YARA Amsoshin tambayoyi

Me ke sa a haifi wasu yara da matsalar ido ta kallon ruduwa wato harari garke, gado ne ko kuwa kuma ko akwai magani ko tiyata?

Daga Haruna Muhammad Katsina

ADVERTISEMENT

Amsa: Harari garke matsala ce ta jijiyoyi masu motsa idanuwa da kan sa ido daya ya daina saiti yayin kallon wani abu. Haka kawai ake haifar wasu yaran da raunin daya daga cikin jijiyoyin idanun. Ba gado ba ne ke nan, tangardar halitta ce wadda za a iya samu tun jinjiri na ciki. Matsalar za ta iya kawo gani bibiyu saboda shi idon mai matsalar ba zai iya karkatowa ya kalli abu cikin saiti ba. Bayan gani bibiyu yakan sa idanuwa su rika yin nauyi ga mai matsalar. To duka wadannan alamu na nauyi da gani biyu-biyu kan iya hana mutum sakat, musamman ma dalibi mai son yawan karance-karance.

A hakikanin gaskiya idan aka ga harari-garke tun a kuruciya ya kamata a fara maganinsa ta hanyoyin tabarau, allura ko tiyata. Idan mutum ya girma da shi matsalar gaba za ta karayi. Don haka dole a ziyarci asibiti tun a kuruciya da zarar an ga yaro na nuna alamun matsalar. ’Yar tiyata ake yi a saita shi daya idon mai raunin, ko a yi tabarau. Zamani ma ya kawo cewa a yanzu akwai allura da ake yi ta sandarar da idon mai hararar, ya tsaya cak, allurer botod, amma ita ma sai ana yi ana maimaitawa duk bayan wasu watanni zuwa shekaru, domin karfinta gushewa yake bayan wani tsawon lokaci.

ADVERTISEMENT

 

Mene ne ciwon ’yar lisuwa?

Daga Zainab Ahmed, Kiru

Amsa: To binciken da na yi ya nuna wannan kalma ta ’yar lisuwa ba wai suna ba ne na wani ciwo, suna ne na alamun wani ciwo a yara. Wasu sukan kira shi da jante ko masassara, wanda duka dai binciken ya nuna yana nufin zazzabi da rama a yara. Zazzabi da rama a yara kuma alamu ne na cututtuka iri-iri a likitance, domin cututtuka da dama kamar su kyanda, tarin fuka da na shika da ciwon kunne da na numoniya da sauransu, wadanda kan addabi yara sukan zo da zazzabi da rama da kin cin abinci.