✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin tambayoyi

Ina da yara har da kanana da ba su barcin rana. In dai suka yi na dare shi ke nan to ba su yin na…

Ina da yara har da kanana da ba su barcin rana. In dai suka yi na dare shi ke nan to ba su yin na rana kamar yadda nake gani a wasu gidajen. Amma dai lafiyayyu ne. Ni ma dai ban cika yin barci sosai ba amma mahaifinsu idan ya kwanta barci da kyar yake iya tashi. Ko shin sun yi gadona ke nan?

Daga Maman Yara

 

Amsa: In dai suna yin na daren mai yawa sosai ya ishe su ba komai, tunda ke ma kin ce lafiyayyu ne, watakila gadon ne kamarki. Ana son kananan yara su samu awa 10 zuwa 15 a cikin awa 24 suna barci ko hutawa dangane da shekarunsu. Don haka idan ba su cika wadannan awanni suna barcin ba dole ki sama musu yadda za su samu awa daya zuwa biyu akalla a yini su kwanta wuri daya ba tare da hayaniya ko surutu ba, koda kuwa ba su yi barci ba kawai su huta, wannan zai kara musu lafiya a kan lafiyar da suke da ita, tunda kin ce lafiyayyu ne.

 

Ni kuma ina da yarinya wadda kullum idan ta dawo daga makaranta sai ta ce kanta na ciwo. Amma a ranakun da ba makaranta ba ta cewa haka, sai ta yi ta wasanta a gida. Ko me ke kawo haka? Akwai shawara?

Daga Maman Muhsin

 

Amsa: Daga irin bayanan da kika zayyana ga alama yunwa ce, domin kin san yunwa na sa ciwon kai. Wato watakila ba ta koshi ne sosai a ranakun da ake zuwa makaranta. Kin san ba duka yara ne ke iya sakin ciki su ci abinci sosai ba a ranakun makaranta saboda sauri kada a makara. To ko da an je makarantar in dai ba a irin makarantun nan ba ce da akan samu ciyarwa sosai to za ta karo yunwa ne. Koda kuwa an ba ta kudin tara ba lallai ba ne su ishe ta sayen abinci mai kosarwa. Idan da kafa ake zuwa makarantar da karin gajiya duka kan taru su sa ciwon kai. Watakila idan kin lura da ta dawo gida ta ci abinci ta huta, ko da ba ta sha magani ba komai zai yi sauki.

 

Ni ce wadda na taba magana a kan haihuwa da na yi sau biyu yaran ba sa zuwa da rai. To ga shi yanzu na shiga shekara ta biyu ko batan wata ban yi ba, shi ne nake so in ji shin ba matsala?

Daga Maryam A.

 

Amsa: Matsala kam akwai ta. Amma tunda kin ce kin taba tambaya a nan watakila an ba ki shawara. Ba mu sani ba ko kin bi ta. Shawarar dai ba ta wuce cewa masu irin wannan matsala dole su nemi likitar ko likitan mata guda su makale masa/mata har sai an nemo masu mafita. Sai dai idan likitan ne ya ce ba mafita, to sai a kara gaba, kamar ya tura ki wurin wani likita na gaba, ko wani asibitin da ya dan dara su.