✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Laifin ‘yan siyasa ne rashin aikin yi ga matasa – Oba na Legas

Oba na Legas, Oba Riliwan Akiolu  wato Babban Basaraken Jihar ya zargi 'yan siyasa da hannu dumudumu kan rashin ayyukan yi ga matasa

Oba na Legas, Oba Riliwan Akiolu  wato Babban Basaraken Jihar ya zargi ‘yan siyasa da hannu dumudumu kan rashin ayyukan yi ga matasa, ya ce ‘yan siyasar kan tara ‘yan jagaliyar siyasa su basu ‘yan kudin da basu taka kara sun karya ba, inda zaka ga irin wadannan matasa basu da aiki sai bibiyar ‘yan siyasar koda yaushe suna ce sai wane.

Sarkin na Legas, ya bayyana haka ne a karshen makon jiya a sa’ilin bikin yaye daliban jami’a Iyamho a jihar Edo.

Ya ce, irin wadannan matasa ‘yan jagaliyar siyasa ba a jihar Edo kadai suke ba suna nan da yawa a sassan kasar nan inda yayi kira gare su da suyi karatun ta natsu su nemi na kansu domin dan abin da suke samu a wajen ‘yan siyasa ba abin dogaro bane, ba abu ne mai matabbata ba, ya ce gwamnati ba zata iya samar wa kowa aiki ba, dan haka ya zama tilas matasa su yi karatun ta nutsu domin ci gaban su da ci gaban ƙasa baki daya.