✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAILATUL – kADRI: Mafificin dare a shekara (1)

Da buwayar mu da girma ikon mu muka saukar da Alkur’ani a cikin dare ‘iko’. Ai daren da ikon mu da sha’anin kudurar mu yake…

Da buwayar mu da girma ikon mu muka saukar da Alkur’ani a cikin dare ‘iko’. Ai daren da ikon mu da sha’anin kudurar mu yake gudana. Ya Muhammadu waya sanar sheka mene ne daren iko? Cewa shi dare ne wanda ibada a cikinsa da tafi alheri daga ibadar watanni dubu wanda babu ‘Lailatul-kadri’ cikin su (daren iko). Cikin wannan dare mala’iku tare da (ruhi) al-Aminu (Jibrilu) wakilin alhaira da albarkatu, suna saukowa suna gaisuwa tare da yin musafaha da muminai suna kuma yi musu addu’a suna nema musu gafara tun farkon daren har ketowar alfijiri”. [Suratul kadari].
A nan ya kamata ga Musulmi ya yi kokarin samun dace da wannan dare mai albarka, wanda yake a cikin 10 karshe na Ramadana, mu zage damtse.
Mu yi kokarin gabatar da ibada da yawaita nafiloli da zikiri da istigfari. wasu sun tafi akan daren ashirin da daya wasu suna ganin yana cikin daren ashiri da uku, wasu suna ganinsa a daren ashirin da biyar wasu suna cewa yana cikin daren ashirin da tara, amma mafiya rinjaye sun tabbatar da shi a daren ashirin da bakwai.
Malam Akawa’i ya ruwaito da Isnadi managarci daga Ibn Umar (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya kasance yana kardadonsa ya kardadance shi a daren ashirin da bakwai”.
Ruwaya ta zo daga Muslim da Ahmad da Abu Dauda da Tirmizi cikin ingancinsu, daga Ubayya dan Ka’abu ya ce: “Na yi rantsuwa da Allah shi ‘Lailatul kadri’ yana cikin watan Ramadana”.
Kuma wallahi nasan kowane dare ne shi na san lokacin da yake aukuwa, shi ne daren da Annabi (SAW) yake umartar mu da mu tsaya masa da yawan ibada, shi ne daren 27, alamun wannan dare kuwa za ka gane shi tun da ranar sa ma’ana ranar sa tana huduwa fara wasai babu wani walwali cikinta.
Ka da ku yi sake cikin neman wannan darare a gaba dayan goman karshe, musamman adararen mara, wadanda muke kaddarasu daga daren 21, 23, 25, 27 da 29 – don koyi da Annabin Rahama (SAW).
A Hadisan Bukhari da Muslim daga Abu Huraira (RA) ya ce; Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda ya tsaya da ibada a daren ‘Lailatul kadri’ yana mai imani da Allah da neman sakamakonsa Allah zai gafarta masa abin da ya aikata na kura-kurai da wadanda ma bai aikata ba”. Mafificiyar addu’a a wannan dare ita ce wadda aka ruwaito daga A’isha (RA) inda take cewa: “Na tambayi Manzon Allah (SAW) cewa idan nasan yau daren ‘Lailatul kadri’ ne kuma ina son addu’a cikin sa me ya kamata in fadi? Sai ya ce;
 ‘Allahumma Innaka Afuwwun Tuhibbul Afwa, Fa’afu Annah”.
Ma’ana: “Ya Allah kai mai yawan yin afuwa ga bayin ka ne, kana son yin afuwa, ka yi mana afuwa”.
AL-ITIKAFI
Ma’anar Al-Itikafi a Shari’a shi ne lazimtar masallaci da zama a cikinsa tare da niyyar neman kusanci ga Allah (SWT).
Hukuncinsa
Shi Sunna ne mai karfi, wadda ake gabatar da ita cikin 10 karshe ta Ramadana. Baya zama wajibi a kan mutum har sai idan ya yi bakancen zai yi itikafin kwana daya ko fiye to wajibi ne akan sa da ya yi saboda fadin Annabi (SAW) cewa: “Wanda ya yi bakance kan zai bi Allah ko zai yi wata ibada, to, lallai ya cika wannan”. Ya zo daga Abu Huraira cewa Umar Ibn Khaddab (RA) ya ce: “Ya Rasulullahi, na yi bakance zan yi itikafin kwana daya a harami – sai Annabi (SAW) ya ce: “Ka cika bakanceka”.
Falalarsa
Itikafi ibada ce mai girma, mai tsari, wanda tsarin ta yake warkar da rai ya da dada zuciya saboda yayewar mutum ga barin wasu abubuwan shagaltarwa da rikice-rikicen duniya, don neman kyakkyawan sakamako na lahira. Ba a yinsa don bukatar duniya, saboda ko yi da Manzon Allah (SAW.
Sharuddan Ingancin I’itikafi
1.  Musulunci – baya inganta ga kafiri.
2.  Bambancewa – Baya inganta ga yaro karami ko mutum maras hankali ko wawa wanda baya bambance mai kyau daga mummuna.
3.  Tsarki – Baya inganta ga mai janaba ko haila ko nifasi – idan janaba ta sami mai itikafi ta hanya mafarki – wajibi ya fito ya yi wanka sannan ya koma. Idan haila ta zo wa mace ko nifasi wajibi ne ta fita daga masallaci, ba za ta komo ba har sai ya dauke sannan ta yi wanka ta koma inda da yalwan lokaci.
4.  Kasancewarsa cikin masallacin da ake Sallar Juma’a, don gudun kada sallar juma’a da tserewa mai ittikafin.
5.  Yin Azumi ga mai itkafi wajibi ne ko na sunnah saboda fadin Sayyida A’isha (RA) cewa; “Sunnar mai itikafi ne ka da ya ziyarci maras lafiya, kada ya halarci jana’iza, kada ya shafi mace ko ya kusance ta, ba zai fita daga masallaci ba sai don bukatar da ta zama babu makawa ga fitar ba a itikafi sai da azumi a baki, babu itikafi sai a cikin masallaci Jami’i.
6.  Nesantar Tarawa Jima’i saboda fadin Allah (SWT).
Allah (SWT) yana cewa: “Kada (ku kusanci matayenku) alhalin kuna masu ittikafi cikin masallatai, wancananka dokar Allah ce kada ku ketara…”
7.  Izinin miji – bai halasta ga mace ta shiga ittikafi ba izinin sa mai gidan ta ba koda ta shiga ba izinin ittakafi bai yi ba. Tana da zunubi sakamakon haka, mai gida yana da hakkin ya hana matarsa, ko ya bata shi in har ta shiga ba izininsa.
Malamai sun yi bayani kan cewa, mata za su iya yin ittikafi a cikin masallatan gidajensu. Ko wani muhalli da suka kebance shi don yin ibadunsu, ba ya yiwuwa acikin dakunan barcin su ko dakunan girke-girkensu, saboda nan ba wurare ne da aka kebance su don yin ibada ba.
Za mu cigaba insha Allah