✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lallana zai koma Southampton

Rahotanni sun nuna dan kwallon Liberpool da ke Ingila, Adam Lallana ya fara shirin komawa kulob dinsa na da wato Southampton a karshen kakar wasa…

Rahotanni sun nuna dan kwallon Liberpool da ke Ingila, Adam Lallana ya fara shirin komawa kulob dinsa na da wato Southampton a karshen kakar wasa ta bana.

Lallana wanda bai dade da dawowa daga doguwar jinya ba, yana buga wa Liberpool kwallo ne a tsakiyar fili.  Sai dai a yanzu ba ya cikin ’yan kwallon Liberpool da ke sahun farko al’amarin da ya sa ba ya wasa a kan kari.

Lallana ya taba zama Kyaftin din Southampton kuma yana daga cikin wadanda suka taimaki kulob din hayewa gasar Firimiya ta Ingila a shekarar 2012 daga rukunin ’yan dagaji.