Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Lalubo kyakkyawar zamantakewa a tsakanin jama’a ita ce a gabanmu – Sarkin Yakin Jihar Yamma

Sarkin Yaqin Yamma Alhaji Salihu Maikankan
Sarkin Yaqin Yamma Alhaji Salihu Maikankan

Sarkin Yakin Jihar Yamma Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan ya yi wani taro na musamman da hakimansa kan matsalolin da al’ummarsa ke fuskanta a sashen inda ya ce, “Muhimmin abin da muka sanya a gaba shi ne lalubo hanyar kyautata zamantakewa a tsakaninmu da sauran jama’a domin zama lafiya da ci gaban kasa. Wannan ne dalilin da ya sa na tabbatar da nadin sababbin hakiman da za su fara aikin isar da wannan sako ga mutanenmu da dukkan masu ruwa-da-tsaki da ke zaune a Kudu maso Yamma.”

Sarkin Yakin ya bayyana haka ne lokacin da yake mika takardar shaidar tabbatar da nadin hakimai 8 da biyu daga cikinsu mata ne a wajen taron da aka yi a fadarsa da ke Iyana Ipaja Agege a ranar Asabar da ta gabata. Ya ce, “Babu wani ci gaba da ake samu idan akwai rikici ko tashin hankali a tsakanin jama’a. Saboda haka nake bukatar ku tabbatar da cewa, kun isar da wannan muhimmin sako wajen wayar da kan mutanenmu game da illarr rarrabuwar kai da ke haifar da bambacin kabila da addini da siyasa da bangaranci da wadansu makiya Najeriya suke amfani da su wajen hargitsa kasa domin cimma burinsu.”

ADVERTISEMENT

Aminiya, ta tambayi Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan game da taron sirri da ya yi da hakiman kafin tabbatar da nadinsu, sai ya ce, “Daya daga cikin muhimmin abubuwan da muka tattauna shi ne su tabbatar da cewa, sun isar da sakon zama lafiya ga mutanenmu da ke zaune a wannan yanki kuma su yi kokarin ganawa da kungiyoyin kabilu da shugabannin al’ummomi daban-daban da za su iya samo muhimman bayanai daga gare su don taimaka mana wajen lalubo mafita game da matsalolin da ke kunno kai tsakaninmu da su.”

Ya jinjina wa Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin kan gudunmawar da yake bayarwa wajen hada kan al’ummar Arewa a jihohi 17 na Kudu. Ya roki hakiman su yi koyi da salon mulki irin na Sarkin Sasa ta fannin hakuri da jama’a a kan irin kalubalen da za su fuskanta.

ADVERTISEMENT

A jawabin wani babban malami a Agege, Sheikh Mu’azu Abdullahi Mu’azu, ya karanto ayoyin Alkur’ani da hadisai da suka yi nuni kan shugabanci na adalci da Annabawan Allah suka yi ta fannin juriya da hakuri da sadaukarwa  har ya suka cimma burinsu na isar da sakon Allah ga jama’arsu. Saboda haka malamin ya yi kira ga sababbin hakiman su yi koyi da Annabawa wajen shimfida adalci da hakuri.

Sababbin hakiman sun hada da Alhaji Lawali Shitu Gulma (Danmaliki) da Alhaji Ibrahim Maikankan (Jarma) da Alhaji Muhammadu Tanko Abubakar (Jakada) da Alhaji Abdulmumini Abubakar (Waziri) da Hajiya Rabi Maikankan (Magajiya) da Hajiya Abu Maikankan (Jakadiya) da Alhaji Adamu Ibrahim (Gayyam) da Alhaji Audu Maji (Makama) da Alhaji Rabi’u Ibrahim (Sarkin Samari) da kuma Alhaji Shehu Mukhtar (Sarkin Gida).

Dimbin jama’a musamman shugabannin kungiyoyin Hausawa da na ’yan kasuwa na ciki da wajen Legas ne suka halarci bikin.