✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lamidon Adamawa ya gargadi shugabanni kan furta kalaman batanci

Mai martaba Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo Mustapha ya gargadi shugabanni kan furta kalaman batanci a tsakaninsu wanda ya ce hakan yana jawo durkushewar kasa.…

Mai martaba Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo Mustapha ya gargadi shugabanni kan furta kalaman batanci a tsakaninsu wanda ya ce hakan yana jawo durkushewar kasa.

Lamidon ya bayyana haka ne a sakon Sallah da ya aike wa al’ummar Musulmin masarautarsa da kasa baki daya. Lamidon ya nuna damuwarsa game da yadda ake garkuwa da mutane da yawan kashe-kashe da yadda matasa ke shan miyagun kwayoyi a wannan zamani.

Ya ce labarai sun iso gare shi cewa matan aure ma ba a bar su a baya ba wajen shan miyagun kwayoyi. Don haka ya yi kira ga Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kara dagewa wajen dakatar da shan miyagun kwayoyi. Sai ya yi kira ga dagatai da masu unguwanni da su hada kai da Hukumar  NDLEA domin shawo kan lamarin.