✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lankwasar labi

Lankwasar labi Lalubar lakabi Lilon li’rabi Lallami da ladabi A dai alkinta adabi   Mikakkiyar hanya Murgudawar juya Muskutawar  kurya Tarden tallafar kwarya Zagaye=-zagayen zirya…

Lankwasar labi

Lalubar lakabi

Lilon li’rabi

Lallami da ladabi

A dai alkinta adabi

 

Mikakkiyar hanya

Murgudawar juya

Muskutawar  kurya

Tarden tallafar kwarya

Zagaye=-zagayen zirya

 

Zabarin zamiya

Zalamar zilliya

Zakwadin zumudin tsiya

Zarge-zargen azargagiya

Zanzaron zaren zargiya

 

Karkarwar katantanwa

Kalume-kalume kanwa

Karon-battar kokowa

Kayi da kifawa

Kilisar salon sukuwa

 

Zirga-zirgar zabi

Zazzafan zazzabi

Zogin kuibi

Zungurun zabi

Zazzagar zubi

 

Tsororuwar tsauni

Tsagwaron tsanani

Tsimayin tsammani

Tsinken tsikaro tsini

Tsalle-tsallen tsakani-tsakani

 

Laulayi laulawa

Langa-langar  laulayawa

Lulun luluwa

Laftun laftawa

Laujen lankwayawa

 

Kwalliyar dubi

Hasken fuska a madubi

Dinka tufafi sababbi

Ai kwalisa ba sababi

A ci dan iccen inabi

 

Kauce-kaucen kurciya

Hargagin hasbiya

Mikar mikiya

Tumbin tunkiya

Kndagarkin kariya

 

Nauyayya da hauhawar kalamai

Kimar manufa takamaimai

Fadar gayauna da maimai

Sana’ar na-duke a daure dammai

Falke ya nunke fama-famai

 

Rabu da rubdugun rububi

Karambanin kinbibi

Bude sabon babi

A cikin kitabi

Akwai hanin aikata aibi

 

Tulelen tumbi

Kululun kusumbi

Tokarar takobi

Kankanbar rikon kanbi

Takun tattaki bi-da-bi

 

Tarin tambayoyi

A allo akwai ayoyi

Akai ai ta yi

Ci gaba da daukar nauyi

Har a daina layi

 

Masana

Ai Magana

Ga alluna

An yi musu zayyana

Don fahimtar maganin fitina

 

Komai a kaishi muhalli

Ba tsangwama balle isgili

Ko tsugudidi tsilli-tsilli

Keke-da-keke ai tozali

Don hana cin zali

 

Na doka dan misali

A fasko masu hankali

Gini a shata shi da tubali

A daina tashin balli

Cikin lumana an warware kulli

 

Rigimar burtali

Dawo da haraji da jangali

Makiyaya ce muhali

Bisdashe dukiyar mai hali

Ai tanadin tattali

 

Lullumin lumana lullum

A daina tada bindiga durum

Balle kwaramniya kwararam

So ake a ji shiru kurum

Bakinku alaikum

 

A tsarin nauyayawa da hauhawar kalmomin kalallame kalamai, don tabbatar da manufa takamaimai, akan yi lankwar lilon li’irabi, don jin dadin Zubi labi-labi. A wani loton ko an tafi a mike babu kanta-karya ko karairaya, sai an lankwaya don sauke kaya. Don haka sai mu bi kafin kayan DAKON DAKON MANGALAR AURA da ake tsiwurwurtawa a wannan zamani, musamman a kasar Haurobiya.

Haurobiyawa a bi hanya mikakkiya, ta yadda batutuwan ingarman karfen karafan titin tarragon kwangirin layin dogo za su kasance babu tawaya. Mu hada karfi da karfe wajen tunkarar balaguron zamani, ta yadda za a nusar da FULLO tsarin kiwon bisashe irin na Danniyar-maki, har ta kai ga ya yi wajen shayarwarsa a masaki, shi ke nan babu sauran hargagi. Su kuwa masu tayar da yamutsi ko da na HARAMTA BOBO DA KWAMBON BOKOKO ne, wajibi ne a himmatu wajen nusar da su cewa sun baude wa tafarkin Mai-duka, Mai-kowa, Mai-komai

Lallai masu wasan Samson-siya-siya da kwakwalwar talakawan kasar ya kamata ku fasko cewa kun kudiri manufofin warware tsilli-tsillin matsalolin al’umma, har ta kai ga an manta da TSAUTSAYIN TSIMAYIN TSALLE-TSALLEN TSAKANI-TSAKANI; ko KWAKWAZO DA KWARAMNIYAR KURUM, al’amarin da ka iya haifar da tashin bindiga durum ko ma ai ta wasan ’yar burum-burum, ta yadda da wuya mutane su ja bakinsu alaikum.

’Yan makaranta masu koyon watsattsake da falle shafukan mujallu da makalu a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, lallai ku kasance masu kakaba wa masu Dawurwurin Dumuiniyar Dama-dama-da-kurda-kurdar siya tagiyar MALAM TUNAU, ta yadda za su yi wurgi da ta MALAM MANTAU, musamman a daidai lokacin da zabi-sonka na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa ke karatowa. Dole ne a ja na-mujiyar wakilan rafkiya, har ta kai ga sun fara famfarar famfare aiki fafur.

Su kuwa Majalisin Tsofaffin kasar Haurobiya, wadda a halin yanzu Saurin-kirinki ke watangaririya da ita, lallai mu rika tabbatar da cewa mun tura masu hankali a jika, ba mahankaltan hannun taguwa ba.

Aiwatar da managartan tsare-tsare, tare da kare-karen hare-hare, shi zai damar mu tsalle shinge haure-haure da hauragiya a kasar Haurobiya.

Gwamnatin Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajon Haurobiya, wajibi ne a taka wa magabtan magabatan, wadanda ke tattakin LANKWASAR LABI a tsarin tafiyar da harkokin al’umma, don tabbatar da LULLUMIN LUMANA LULLUM; a daina KWARAMNIYA KWARARAM, don so a ke a jiSHIRU KURUM; kowa ya ja BAKINSA ALAIKUM!

Lallai ’yan watanda, wadanda ba sa kishin kasa, sai kisisinar kishiya kamata ya yi a hana su Zabarin zamiya da Zalamar zilliya da Zakwadin zumudin tsiya da Zarge-zargen azargagiya da Zanzaron zaren zargiya, ballantana su karke da Karkarwar katantanwa da Kalume-kalume kanwa da Karon-battar kokowa, har ai Kayi da kifawa ko Kilisar salon sukuwa!

Jiki dai magayi bankar hayakin bukin tunkurar Dan-Korau!