Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Legas ta Gabas: Har yau ba mu da dan takara -APC

Legas ta Gabas: Har yau ba mu da dan takara -APC

Jam’iyyar APC reshen Jihar Legas ta ce har yanzu ba ta da dan takarar maye gurbi Senatan Legas ta Gabas, Sikiru Adebayo Osinowo, wanda ya rasu cikin watan da ya gabata, wanda hakan ya bar gurbin da za a cike.

A takardar da hannun Kakakin Jam’iyyar a jihar, Seye Oladejo, ya karyata rade-radin cewar tsohon kwamishinan watsa labarai na Legas, Dele Alake suka zaba a matsayin dan takara.

Ya ce hakan ba gaskiya ba ne kuma ba su fara maganar zaben dan takara ba.

Ya ce har yanzu jam’iyyar na juyayin rasuwar Sanata Sikiru Adebayo Osinowo ne, wadda ta saka jam’iyyar cikin halin jimami.

Ya kuma kara da cewar har yanzu hukumar zaben ba ta sanar da jam’iyyar takamaiman lokacin da za a gudanar da zaben maye gurbin ba.

Takardar ta bayyana cewar: “Kundin tsarin mulkin jam’iyya ya fayyace hanyoyin da ake bi na zabar dan takarar da zai wakilce ta a zabe, kuma da shi za mu yi amfani. Zaben dan takarar zai kasance na sasanci ko yar tunke.

“Jam’iyya na sane da ra’ayoyin da zaben ka iya haifarwa a matsayin ta na jam’iyyar mai ci, amma muna rokon kowa ya bi ka’idodin da aka gindaya.

“Muna kuma kara tabbatar da kokarinmu na gudanar da zaben bisa adalci ga wadanda suka nuna sha’awar shiga.

“Muna so mu shaida wa ‘yan jarida da ‘yan jam’iyya da mata da duk wadanda ke da hakki a zaben cewar, zamu sanar da su lokuta da tsare-tsaren da muka yi na gudanar da zaben a lokacin da ya dace”, Kamar yadda takardar ta fitar.