Da Dumi Dumi

Leicestery City za ta hana Ndidi buga wa Super Eagles kwallo

Rahotannin da ke fitowa daga kulob din Leicester City na Ingila sun nuna akwai yiwuwar mahukunta kulob din su hana Wilfred Ndidi dan asalin Najeriya buga wa Super Eagles kwallo a watan Maris.

Ndidi, wanda yanzu yake jinya saboda raunin da ya samu, ana sa ran zai koma fagen wasa ne a karshen watan Fabrairun bana.

A ranar Talata mai zuwa ce ake sa ran za a yi jadawalin neman zuwa gasar cin Kofin Afirka a Masar inda Kungiyar Super Eagles za ta san kungiyoyi uku da rukunin da za ta fafata.  Ana sa ran za a fara gudanar da wasannin zagayen farko a tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Maris mai zuwa wanda hakan ya sa Leicester City take ganin da wuya ta kyale Ndidi ya yi wa Super Eagles kwallo.

Ndidi yana daga cikin ’yan kwallon da tauraruwarsu ke haskakawa a kulob din Lericester City a bana.  Sai dai ba a sani ba ko kungiyar Super Eagles za ta amince da wannan mataki da Leicester City take shirin dauka  a kan Ndidi.

ADVERTISEMENT
Share