✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lere ta shirya yaki da masu sayar da miyagun kwayoyi

Shugaban Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Alhaji Abubakar Buba ya bayyana cewa karamar hukumar tasa ta shirya, domin ganin ta yi yaki da…

Shugaban Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Alhaji Abubakar Buba ya bayyana cewa karamar hukumar tasa ta shirya, domin ganin ta yi yaki da masu sayar da miyagun kwayoyi a yankin.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake mikawa wasu matasa 10, da karamar hukumar ta tura suka je suka koyo sana’o’i kayayyakin sana’o’in da suka koyo tare da tallafin kudade a garin Saminaka.

Ya ce ganin yadda matasan yankin suke fuskantar matsalar rashin aikin yi, wadda take jefa su cikin matsalar shiga shaye-shayen miyagun kwayoyi.

“Don haka wannan karamar hukumar ta ga cewa ya kamata ta tashi ta yi yaki da wannan mummunar dabi’a ta sayar da miyagun kwayoyi a  yankin, domin ceto rayuwar matasanmu a wannan yankin. Kuma kashi 80 cikin 100 na masu sayar da miyagun kwayoyi a yankin baki ne. Don haka ba zai yiwu karamar hukumat ta bar baki su rika zuwa suna shigo da miyagun kwayoyi suna sayarwa matasan yanki ba,” a cewarsa.

Abubakar Buba ya nuna farin cikinsa kan kokarin da matasan karamar hukumar 10 suka yi a wajen da aka tura su koyo sana’o’in. “Wadannan matasa sun kware kan sana’o’in man shafawa da dinki  da kafinta da yin jakankuna da suka koyo. Karamar Hukumar Lere zata tallafawa wadannan matasa domin karfafa masu gwiwa, su cigaba da gudanar wadannan sana’o’i da suka koyo. Domin su gina kansu su gina wadanda suke karkashinsu”.

Abubakar Buba ya yi bayanin cewa kowace Karamar Hukuma a Jihar Kaduna, ta tura mutum 10 don su je su koyi sana’o’i a Jami’ar Jihar Kaduna. Don haka ne aka tura wadannan matasa 10, suka je suka  koyo wadannan sana’o’i daban-daban.

Ya ce manufar shirin shi ne tallafawa matasa su koyi sana’o’i kuma a basu jari su fara aiki domin su je su koyawa wadansu. Domin a rage zaman banza da matasa suke yi, a Jihar Kaduna.

Ya yi kira ga al’ummar Karamar Hukuma su yi siyasa cikin kwanciyar hankali. Ya ce kowa ya je ya yi ra’ayinsa ba tare da batanci ko zage-zagen juna ba. Da yake jawabi a madadin matasan, daya daga cikin matasan da suka koyo sana’o’in, Malam Abdullahi Idris Mariri  ya bayyana tabbacin cewa da yardar Allah, zasu je su bude wurare domin su ci gaba da aiwatar da wadannan sana’o’i da aka koya masu. Kuma su koyawa wadansu. Daga karshe karamar hukumar ta tallafawa wadannan matasa da kudi naira dubu 20 kowannensu.