✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool tana zawarcin dan kwallon Najeriya Victor Osimhen

Kulob din Liverpool da ke Ingila ya kammala shirin sayen dan kwallon Najeriya Victor Osimhen kamar yadda kocin kulob din Jurgen Klopp ya sanar  a…

Kulob din Liverpool da ke Ingila ya kammala shirin sayen dan kwallon Najeriya Victor Osimhen kamar yadda kocin kulob din Jurgen Klopp ya sanar  a ranar Talatar da ta wuce.

Kulob din ya ce zai yi zawarcinsa ne da zarar an bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a wannan wata na Janairu.

Victor Osimhen wanda ya sanya wa kulob din Lille na Faransa hannu a watan Yunin bara, kawo yanzu ya zura kwallo 13 a raga a dukkan wasannin da ya yi wa kulob din a kakar bana.

Osimhen wanda tauraruwarsa ke haskakawa a bana, kulob da dama suna rububi a kansa da suka hada da FC Barcelona na Spain da Tottenham da Chelsea da kuma Liverpool dukkansu a Ingila da sauransu.

Osimhen yana daga cikin matasan ’yan kwallon da za su fafata a Gasar Gwarzon Matashin Dan Kwallon Afirka ta bana a ranar Talata mai zuwa a Masar.