✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liberpool ta sanya farashin Fam miliyan 55 a kan Suarez

Kulob din Liberpool da ke Ingila ya nanata kudurinsa na sayar da shahararren dan kwallonsa Luis Suarez ga kulob din Real Madrid da ke Sifen…

Kulob din Liberpool da ke Ingila ya nanata kudurinsa na sayar da shahararren dan kwallonsa Luis Suarez ga kulob din Real Madrid da ke Sifen muddin kulob din ya amince zai biya Fam miliyan 55 kwatankwacin Naira biliyan 1 da Miliyan 430.  Kulob din ya ce akwai yiwuwar zai sayar da dan kwallon a watan Janairu mai zuwa idan aka bude kakar saye da sayar da ’yan wasa.
Shi dai Suarez, dan asalin kasar Uruguay, a kakar wasan da ta gabata ne ya yi yunkurin canza sheka daga Liberpool zuwa Madrid amma abin ya ci tura.  A wancan lokaci cinikin bai kaya ba, ganin yadda kulob din Madrid ya kashe fiye da Fam miliyan 86 wajen sayo Gareth Bale daga kulob din Tottenham na Ingila.
Sai dai ga dukkan alamu kulob din biyu sun yi yarjejeniya ce a tsakaninsu cewa cinikin zai kaya ne idan ba su tabuka abin-a-zo-a-gani a watan Disamba mai zuwa ba. Wakilin Suarez mai suna Pere Guardiola ya yi farin ciki da wannan yarjejeniya.
Akwai yiwuwar kulob din Arsenal da ke Ingila shi ma ya shiga batun cinikin don yana daga cikin kulob din da ke zawarcin Suarez.  Kulob din Liberpool ya gwammace ya sayar da Suarez ga wani kulob daban fiye da na Arsenal da yake dauka a matsayin abokin adawa.
Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya nemi Suarez a kakar saye da sayar da ’yan kwallon da ta gabata amma ganin hakarsa ba za ta cimma ruwa ba ya canza shawara inda ya saye dan kwallon Madrid Mesut Ozil a kan Fam miliyan 42 da rabi.