✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Libya: Sojin Khalifa Haftar sun karbe iko da birnin Sirte

Dakarun da ke biyayya ga Babban Hafsan Sojin Basar Libya, Khalifa Haftar sun ce sun karbe iko da birni mai muhimmanci na Sirte, daga gwamnatin…

Dakarun da ke biyayya ga Babban Hafsan Sojin Basar Libya, Khalifa Haftar sun ce sun karbe iko da birni mai muhimmanci na Sirte, daga gwamnatin da Yammacin  Turai ke mara wa baya a Tripoli.

“Mun bwace baki dayan garin Sirte daga hannun ’yan ta’adda, inji Ahmad al-Mesmari, wani mai magana da yawun mayaban Janar Khalifa Haftar yayin da yake bayani a talabijin.

Tripoli dai ba ta yi wani sharhi a kan lamarin ba, haka kuma babu cikakken bayani a kan gwabzawar.

Sirte da ke kan gabar tekun Meditareniya, birni ne mai muhimmanci, domin kuwa dakarun na Haftar ne da ikon gabashinsa, yayin da Tripoli take iko da yankin har zuwa yammacinsa.

Sirte shi ne garin haihuwa na tsohon Shugaban Basar marigayi Muammar Gadhafi, kuma ya yi zama a barbashin Bungiyar IS, kafin gwamnati ta bwato shi daga hannun masu tsattsauran ra’ayin addini, tare da goyon bayan Amurka. Tun 2016 da aka kori IS, Sirte ke barbashin ikon gwamnatin Tripoli da Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya. ’Yan tawayen da ke biyayya ga Janar Khalifa Haftar, sun dade suna kai farmaki da nufin bwace iko da Tripoli babban birnin Libya.

Libya ta dade tana fuskantar tashe-tashen hankali tun lokacin da aka hambarar da Gadhafi aka kuma kashe shi a shekarar 2011. Duk bobarin daidaita siyasar basar ya tashi a tutar babu.

Bangarorin biyu suna yabi da juna ne don neman iko da Tripoli tun a watan Afrilu, lamarin da ya rutsa da dubban fararen hula.

Wani mazaunin garin na Sirte ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa sun ga jerin gwamman motocin mayaban a lokacin da suke ta sinitiri bayan bwace garin.

A yanzu haka sune ke ribe da yawancin garuruwan Libya, sai dai ban da wasu muhimmai da suka hadar da Tripoli inda nan gwamnatin da suke yaba ta yi sansani.

Birnin yana kusa da yankin Crescent mai arzikin mai. Tun kawar da Kanal Ghaddafi, Libya ke fama da yabi.