✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Libya ta sake maido da ‘Yan Najeriya 195 gida

An sake maido da wasu rukunin ‘yan Najeriya 195 gida daga kasarLibya.  Wannan adadin na daya daga cikin jigilar mai yawa da aka maido su…

An sake maido da wasu rukunin ‘yan Najeriya 195 gida daga kasarLibya.  Wannan adadin na daya daga cikin jigilar mai yawa da aka maido su gida a cikin jirgi guda tun lokacin da aka fara jigilar a shekarar 2017.

Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) tare da wasu jami’an gwamnatin tarayya ne suka karbi wadanda aka dawo da su, a filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas.

Cikin mutum 195 da aka dawo da su akwai mata da adadinsu ya kai 113 ciki akwai ‘yan mata da yara da masu juna biyu, sai kuma maza da adadinsu ya kai 82 wadanda suka hada yara da matasa.