✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Libya ta shiga matsalar wutar lantarki da dogon layin sayen man fetur

kasar Libya ta fara sayen man fetur daga kasashen waje, kuma dogon layin sayen mai yana ta karuwa, al’amarin da ya jefa rayuwar al’ummar kasar…

kasar Libya ta fara sayen man fetur daga kasashen waje, kuma dogon layin sayen mai yana ta karuwa, al’amarin da ya jefa rayuwar al’ummar kasar cikin mawuyacin hali, ga kuma rikicin siyasa. Wutar lantarkin Libya ta ragu da kimanin megawatt dubu.
Mafi yawan wuraren hakar mai da ke yankin Gabashin kasar, sun daina bayar da man ga cibiyoyin samar da wutar lantarki. Wannan dai ita ce mummunar matsalar da kasar ta samu kanta, tun bayan yakin basasar da aka yi a shekarar 2011.
Babban birnin Libya, Tripoli na fama da matsalar wutar lantarki, don haka za a rika raba wutar. “daukacin cibiyoyin samar da iskar gas da ke gabashin kasar, duk an daina aiki a cikinsu,” a cewar wani jami’i.
Ahmad Mustapha Hussein, wani babban jami’in Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Libya, ya bayyana cewa za a dauki makonni kafin na’urorin sarrafa iskar gas su koma kan aiki yadda aka saba.
Shi kuwa Ministan Harkokin Mai, AbdelBari Arusi, ya bayyana cewa kafin a yamutsa Libya, kasar na samar da albarkatun iskar gas har kubic mita biliyan biyu da miliyan 400.