✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likita mai hanzari

Assalamu alaikum Manyan Gobe. Yaya karatu? Tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “Likita mai hanzari”. Labarin ya yi…

Assalamu alaikum Manyan Gobe. Yaya karatu? Tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “Likita mai hanzari”. Labarin ya yi nuni ne ga illar yin hanzari ko gaggawa. A sha karatu lafiya.

 

An yi wani likita a wani kauye. Likitan ya kasance mai yawan kai ziyara gidajen marasa lafiya. Da yake ciwo ya fi  tsanani da dare, hakan ya sa likitan ya fi yin fitar dare  don duba marasa lafiya a kauyen.

Ran nan sai hadari ya hadu, matarsa na ganin haka sai ta ba shi shawarar kada ya fita zuwa duba marasa lafiya har sai ruwa ya yi sauki.  Nan likitan ya ki amincewa da hakan inda ya fita a cikin daren.

An tafka ruwa da walkiya da tsawa amma hakan bai hana shi canja shawara ba. Nan dai ya fita cikin duhu yana haska tocila.

Yana cikin tafiya sai kafarsa ta makale a cikin wani rami wanda hakan ya sa ya ji ciwo.  Da kyar da jibin goshi ya koma gida saboda raunin da ya ji.  Ga shi bai kai inda ya yi niyyar zuwa ba, sannan ga shi ya ji ciwo wanda hakan ya tilasta masa komawa gida.

Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labari.