✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likita ta ciro tsaka mai rai da ta kwana biyu a kunnen wani

Wata likita mai suna Baranya Nganthabee, ta bayyana irin abin mamakin da ta ce, ba za ta taba mantawa da shi ba, a matsayinta na …

Wata likita mai suna Baranya Nganthabee, ta bayyana irin abin mamakin da ta ce, ba za ta taba mantawa da shi ba, a matsayinta na  likitar asibitin Rajabithi a garin Bangkok babban birnin kasar Thailand inda aka samu wata tsaka da ke rayuwarta a cikin kunnen wani mara lafiya.

Wannan matashiyar likitar ta wallafa wannan abin mamakin a shafin sada zumuntarta na Facebook. Ta ce har ta fara shirin ajiye aikinta tun ranar da wani mara lafiya ya ziyarci asibitin da take aiki ya fara bayyana abin da ke damunsa na tsananin ciwon kunne wanda yake hana shi sukuni har zuwa kwana biyu.

A lokacin da likitar ta yi amfani da na’urar daukar hoton cikin kunne, Baranya ta firgita game da abin da ta gani, inda ta ga wani abu na yawo a cikin kunnen, sai ta diga wani magani a cikin kunnen ta umarci mara lafiyan ya karkatar da kunnensa ta yadda duk wani abu da ke ciki zai yi waje da kansa.

Amma duk da haka abin ya ci tura har sai da ta yi amfani da karfen fitar da karamin abu ta ciro tsakar da ke yawo a cikin kunnen, daga nan ta gano lallai ba kwaro ba ne a cikin kunnen tsaka ce, wanda ake kira ‘Jing Jok’ a kasar Thailand.

Baranya Nganthabee, ta wallafa cewa da farko ta yi tunanin karamin kwaro ne a cikin kunnen, sai daga bisani ta gano ai tsaka ce mai rai wadda take yawo a cikin kunnen. “Na yi tunanin wannan shi ne ranar karshen aikina a asibiti, saboda yadda na firgita ta yadda har tsaka mai rai za ta samu damar shiga ramin kunnen mutum.

Bayan an ciro tsakar daga cikin kunnen, likitar ta dada yin binciken cikin kunnen mara lafiyan sosai don tabbatar da babu wani bangaren jikin tsakar da ya rage a cikin kunnen wanda zai iya zama ciwo nan gaba, amma sai aka yi nasara komai ya yi yadda ake bukata kuma marar lafiyan a yanzu yana cikin koshin lafiya.

Likitar dai ta dade tana jimamin yadda wannan ’yar tsakar ta rayu a cikin ramin kunnen mutum har na kwana biyu.