✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likita ya gusar min da hankali ya yi min fyade – Matar aure

Kazafi ne kawai don ta bata min suna – Likita An zargi wani likita mai suna Dokta Tijjani Ahmad Faruk da yi wa wata matar…

  • Kazafi ne kawai don ta bata min suna – Likita

An zargi wani likita mai suna Dokta Tijjani Ahmad Faruk da yi wa wata matar aure fyade bayan ya rufe mahaifarta, lamarin da ya rikita tunanin jama’a a Jihar Sakkwato.

Aminiya ta zanta da lauyan matar (an sakaya sunanta) da ake zargin an yi wa wannan aika-aikar don jin yadda lamarin ya faru.

Barista Muhammad Mansur Aliyu lauya ne da ke karkashin cibiyar lauyoyi ta Sadik and Co, ya ce “Matar da mijinta ne suka same ni da korafi kan wannan likita da yake aiki a Asibitin Mata na Maryam Abacha suna zargin ya yi mata allurar barci kuma ya yi fyade bayan ya rufe mata mahaifa. Na tambaye ta yaya haka ta faru, ta ce bayan aikin cire karin mahaifa (Faboraits)  da aka yi mata a Asibitin Maryam Abacha wata biyu da aikin, likitan ya kira mijinta ya turo masa ita zai yi wani bincike, a Juma’a ne ya kira shi ya tura ta a ranar Asabar da ta je ofishinsa ya tura ta dakin tiyata ya shiga da ita kurya sosai in da ba mutane, ya yi mata allura yana wasu gwaje-gwaje a jikinta da allurar ta fara kama ta ce ya ce ta tashi ta je. Ya kira wata mata ta rike ta ta kai ta dakin hutawar likitoci (common room), kafin ta shiga ne hankalin ta ya dauke ba ta farka ba sai kusan Magariba da ta farka ta gan shi gefenta, kuma ta ga alamun an sadu da ita. Sai ta tambaye shi me ya sa zai yi mata haka?  Sai ya ba ta hakuri ya ce kada ta gaya wa mijinta don in ya sani aurenta na iya mutuwa, ya ba ta Naira 1000 ta hau Keke NAPEP. Ta ce me za ta fada wa mijinta ba takarda ba magani, ya ce zai kira mijin.”

Lauyan ya kara da cewa, “Ba ta gaya wa mijin ba a lokacin, daga baya ne al’adarta ta rika yi mata wasa, ta dauki wata uku ba ta zo ba, a gwada ba ciki ba ne, suka tafi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo aka yi mata gwaje-gwaje da hotuna, aka sake cewa ta je Zifafi a yi mata wani hoton bayan nan ne  da sakamakon hoto ya fito likitocin suka fada mata ita da haihuwa har abada. A nan ne hankalinta ya tashi ta zaci allurar da ya yi mata ne, sai ta sanar da mijin ya yi mata allurar gushewar hankali.”

Lauyan ya ci gaba da cewa “Ba ta sanar da mijinta Dokta ya yi mata fyade ba sai bayan ta zo wurinmu, muna neman shaidar yadda za a iya sanin Dokta ya yi wasa da aikinsa ya zalunci marar lafiya. Ga shi babu wata shaidar an yi lalata da ita, a doka fadin mace kawai bai yi a kotu dole sai da shaida. Ni na ce ta kira likita a waya ko ma samu shaida mun yi nasara ta dauki muryarsa a hirarsu ta shigar da maganar bai musanta ba, ina da daukar zan sanya maka ka ji. Daukar da muka yi ba ta da inganci sosai. Sai na ce ta je ofishinsa ta dauko mana muryarsa aka ba ta babbar waya, haka aka yi a hirarsu ya aminta ya yi lalata da ita.”

Lauya Mansur Aliyu ya ce “A tsarin doka ga abin da ya yi muna da zabi uku ko mu kai kararsa a wurin ’yan sanda su kama shi, ko a rubuta wa hukumar da ta ba shi shaidar zama likita ta zo ta bincika in yana da laifi a soke shaidarsa ta zama likita, ko mu rubuta korafi ga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Sakkwato don ma’aikacinta ne. Mun fara da ma’aikatar, mu ga abin da za ta yi in ba ta dauki mataki ba za mu kara gaba.”

Ya ce sun yaba wa Kwamishinan Lafiya, saboda suna mika kukanmu kwana daya aka kira su kan maganar, Kwamishina ya kafa kwamiti suka fuskanci kwamiti shi da matar da mijinta da Dokta Tijjani. “Ta fadi komai yadda suka yi, ta yi rantsuwa a matsayinta na Musulma cewa Dokta ya yi lalata da ita ba tare da son ta ba, har ta ce in ta yi masa karya ko kazafi kada Allah Ya ba ta abin da take so. Aka ba shi dama ya yi magana a karshe dai ya yarda ya sadu da ita,” inji shi.

Ya ce “Babu wata doka a likitance da ta yarda da huldar waje da marar lafiya mace da likita, balle a cikin asibiti a keta haddin mace a nuna sonta, in ma da amincewarta akwai hukunci don wannan aikin laifi ne mai girma.”

Barista Mansur ya zargi wadansu yadda kafafen wasat labarai suka ki daukar labarin don sun hada baki da Ma’aikatar Lafiya saboda ba su son labarin ya fita. Ya ce tafiyar hawainiya da ya ga ana yi ne a lamarin ya sanya ya sanar da wani dan jarida ya dauka ya sanya a jaridarsa ta Intanet.

Mijin matar mai suna Alhaji Shehu ya shaida wa Aminiya cewa “Likitan ya ci amanarmu kuma ya ci amanar Musulunci don mu amana muka ba shi ya ci, mijin kanwar matata ce da yake aiki a Asibitin Kwararru ya hada mu da shi kan zai yi mata aiki don ya san wahalar da muka sha a Asibitin Koyarwa na Dan Fodiyo kan matsalar da ta samu na yin cikin bayan mahaifa da kuma mutuwar yarinya a cikinta kafin haihuwa.”

Ya ce dangantakarsu da yadda duke da shi ba su yi tsammanin zai cutar da su ba, “Ya yi wa matata aikin da ba shi ne na sanya hannu a kai ba, ya kira ni a ranar Juma’a a waya yana son in tura ta ya yi mata bincike, na tura ta ranar Asabar da safe, na kira ta da rana ba ta dauka ba, ni ban zaci komai ba, don wurin da na tura ta, akwai alaka tsakaninmu, ashe shi yana da mummunan nufi gare mu.” inji Shehu.

Ya ce “Na yarda da matata ba za ta zalunce ni ba Likita ya ci amanar Musulunci, Wannan jarrabawa ce daga Allah na karba ina tare da matata har abada. Sai bayan wata takwas da yin wannan aika-aikar asiri ya tonu.”

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Dokta Tijjani Ahmad da ake zargi inda ya ce lauyansa ne ke da hakkin magana kan lamarin.

Sai da Aminiya ta tuntubi lauyan likitan Barista Muhammad Nuhu ya ce, “Wani ma’aikacin jinya ne ya kawo su wurin Dokta Tijjani a taimaka musu aka yi mata aiki. Ba gaskiya ba ce su ce aikin da aka yi mata ba don shi ne ta zo asibitin ba.”

Ya ci gaba da cewa “Da ta samu matsalar samun juna biyu bayan mahaifa an yi mata aiki a gefen hagu na mahaifa a Asibitin Koyarwa na Usman Danfodiyo. Da ta zo wajen su Dokta da wasu hotuna da aka yi mata na gwaji aka ga lallai cutar da take fama da ita, sai an yi mata aikin a gefen dama na mahaifa, mijinta ya aminta ya sanya hannu, duk wanda a likita ya san in aka yi aiki ga mahaifa dama da hagunta ba yadda za a yi a sake samun haihuwa, shi ne abin da ya same ta.”

Ya ce a je a dubi takardun sirrin na bayanan asibiti za a ga abin da suka sanya hannu, likita ba ya yin aiki shi kadai.

“Ta ce ya yi mata allura ba shi yake allurar nan ba Nasi ne ke yi, likita ba ya samun dama shi kadai da marar lafiya duk wanda ke asibiti ya san da wannan. Ba inda ya ce ya yi amfani da ita, kamar yadda suke fadi kawai tana son su bata masa suna ne. Allah ne kadai Ya san abin da ke cikin ranta take son bata wa Dokta Tijjani suna. Me ya sa ba ta yi korafi wurin ’yan sanda ko ta tafi kotu ba ta je wurin Kwamishina, in an yi mata fyade ne? In ba ta je kotu ba mu za mu tafi kotu, kuma ’yan jaridar da suka yi labari ba su ji ta bangarenmu ba, za mu kai su kotu,” inji Barista Muhammad Nuhu.

Da Aminiya ta tuntubi Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato, Dokta Muhammad Ali Inname don sanin bayanin da kwamitin da ya kafa kan lamarin ya gano da halin da ake ciki, ya ce Babban Sakataren Ma’aikatar ne zai yi magana kan lamarin don shi ne ya fi dacewa ya yi magana a kan lamarin.

To amma da wakilinmu ya tuntubi Babban Sakataren sai ya ce ba zai yi magana ba sai ta hannun Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar.

Da Aminiya ta tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Alhaji Ibrahim kan maganar ya ce zai tuntubi wakilinmu, amma kuma bai tuntube shi ba. Kuma da ya sake kiransa ta waya a jiya Alhamis, sai ya ce a jiyan ne za su yi zaman karshe don fitar da sakamakon abin da suka gano, kuma zai sanar da wakilnmu halin da ake ciki. Sai dai har zuwa kammala wannan rahoto ba su fitar da matsayar ba.