Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Likitar bogi ta sace jaririyar kwana uku a asibitin Filato

Mahaifin wata jaririyar ’yar kwana uku mai suna Nwa God Chukwuebuka mai shekara 33 da matarsa Mary Chukwuebuka mai shekara 30 sun shiga cikin tashin hankali bayan wata mata da ba a san wace ce ba ta  sace jaririyar da suka haifa a Babban Asibitin Filato kwana uku kacal da haihuwarta.

Mahaifan jaririyar sun shaida wa ’yan jarida a shekaranjiya Laraba cewa matar ta haifi jaririyar lami lafiya a ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata, yayin da wata likitar bogi ta sace jaririyar a ranar  31 ga watan Mayun.

ADVERTISEMENT

Madam Mary ta ce ta sha matukar wuya kafin ta haifi jaririyar abin da ya sa aka kwantar da ita ana yi mata karin jini.

“A ranar Alhamis da yamma ne wata mata ta same ni sanye da kayan likita a matsayin ita ma likita ce a asibitin. Sai ta nemi in ba ta fom din da likita ya ba ni don a yi mini wasu gwaje-gwaje, amma da na mika mata sai ta ce ba fom dina  take so na ba ta ba, fom din da za a yi wa jaririyar gwaje-gwaje.  Sai na shaida mata ai likita bai ce a yi wa jaririyata wasu gwaje-gwaje ba, don ita lafiyar lau take.  Sai ‘likitar’ ta ce ai tilas a yi wa jaririyar wasu gwaje-gwaje.  Ganin ita ma likita ce sai na amince ta tafi da jaririyar,” inji ta.

ADVERTISEMENT

“Ganin wannan shi ne haihuwata ta farko sai mahaifiyata ta bi ‘likitar’ wajen yin gwaje-gwajen amma sai ta bukaci ta koma kuma ta yi alkawarin maido da jaririyar da zarar an kammala.  Tun daga lokacin ba mu sake gani ko jin duriyar matar ko jaririyar ba,” inji Mary.

Shugaban Asibitin Dokta Philimon Golwa ya tabbatar da aukuwar lamarin.  Sai dai ya ce suna gudanar da bincike don gano yadda abin ya faru.  Ya ce suna zargin akwai lauje cikin nadi ganin yadda mahaifan jaririyar suka ce an sace ta amma ba su sanar da mahukunta asibitin ba sai bayan kimanin awa daya.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato DSP Tyope Terna ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ba zai ce uffan ba sai bayan an kammala bincike.