✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun ciro duwatsu da murafen kwalba da tsabar kudi daga cikin wani

Wani dan kasar Koriya ta Kudu da ke jinya a asibiti sanadiyyar matsanancin ciwon ciki, likitocin asibitin sun gano duwatsu da murafen kwalba da karfunan…

Wani dan kasar Koriya ta Kudu da ke jinya a asibiti sanadiyyar matsanancin ciwon ciki, likitocin asibitin sun gano duwatsu da murafen kwalba da karfunan kudi a cikinsa da nauyinsu ya kai kilo 2.

Mara lafiyan mai shekara 54 ya fara jinya a asibitin ne bayan ya fara jin ciwon ciki, daga nan ne likitocin suka fara yi masa gwajin cututtuka don tabbatar da abin da ke damunsa.

A lokacin da mara lafiyan ya je asibitin, kafin likitocin su yi masa gwaji idan suka taba cikinsa sai su rika jin wata alama kamar duwatsu a ciki. Hoton na’urar likitocin ne ya tabbatar da akwai abubuwan da suke sanya marar lafiyan ciwon ciki, wadanda suka hada da duwatsu da karafuna.

A lokacin da likitocin suka gano abubuwan da ke cikin marar lafiyan sun yi matukar mamaki, ganin yadda aka ciro murafen kwalba da karfunan kudi a cikin mutumin wanda suka ce, ya kai nauyin kilo 2 da aka auna.

Rahoton mujallar Amurka ta American Journal of Medical Case Reports ta fitar wanda Dokta Pyong Wha Choi ya wallafa ya ce, ba a cika samun irin wannan al’amari ba. A cewar rahoton mara lafiyan ya hadiye duwatsun ne da nufin kawar masa da juyayin abin da ke damunsa a rayuwa, binciken na nuna cewa, ya hadiye wadannan abubuwa ne a tsawon lokaci

A lokacin da aka tambayi mara lafiyan kan yadda lamarin ya faru ya ce, yana hadiyewa ne duk lokacin da yake cikin damuwa, sai dai wani lokacin yana  shan kwaya don samun natsuwa.

Mutumin dan garin Goyang ta Gabas a babban birnin Seoul da ke kusa da iyakar kasar Koriya ta Arewa, an ce, asalin mutumin an haife shi da tabin hankali.

Da farkon yi wa marar lafiyar tiyatar, likitocin sun yi amfani da bututu suka zura a cikin bakinsa zuwa cikinsa, amma ba a samu nasarar tiyatar ba saboda yawan abubuwan da mutumin ya hadiye.

A rahoton da Dokta Choi ya wallafa bai bayyana adadin yawan abin da mutumin ya hadiye ba. Amma tiyatar da aka yi masa wadda aka samu nasarar an bi matakai daban-daban.

An sallame shi daga asibitin jami’ar Inje a Ilsan Paik bayan jinyar kwana 9.

Dokta Choi ya ce, irin wannan lamarin ya fi faruwa ne ga kananan yara, yayin da matashi kuwa sai dai ya hadiyi kashi ko kifi ta hanyar kuskure.