Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Likitoci sun ciro hakora 526 daga bakin dan shekara 7

Likitocin asibitin hakora na Sabeetha a Chennai da ke Kudancin Indiya, sun gamu da abin mamaki bayan wani yaro mai kimanin shekara bakwai ya bayyana musu ciwon bakin da yake yi, sai suka yi masa gwaji ta hanyar amfani da na’urar daukan hoton jikin dan Adam, sai dai sakamakon da suka samu ya nuna bakin yaron cike yake da hakora sama da dari.

Likitocin sun yi nasarar ciro hakora har 526 daga cikin bakin yaron wannan shi ne karon farko da aka gano ciwon bakin da yake damun yaron bayan ya shafe kwanaki yana fama da matsanancin ciwon baki.

ADVERTISEMENT

Yaron mai suna Rabindran, an kai shi wani asibiti mai zaman kansa sakamakon fama da yake da matsanancin ciwo da kumburi a dasashinsa.

ADVERTISEMENT

Da farko mahaifin Rabindran, mai suna Parbhu mai kimanin shekara 40 da mahaifiyarsa Rajakumari mai shekara 33 sun yi tunanin ko yaron na fama da cutar amosanin jini ne (kansa) a dasashinsa, har sai da suka kai shi asibitin hakora na Kwalejin Sabeetha da ke Chennai a Kudancin Indiya sannan suka fahimci ciwon da yake damun dansu.

Likitocin asibitin sun yi matukar mamakin abin da ke cikin bakin yaro sakamakon binciken da suka yi ta hanyar amfani da ‘CT Scan’ da ‘D-ray’ don gano abin da ke damunsa, a nan ne aka gano yawan hakora sama dari da suka cika bakin ne suka haddasa tsananin ciwon.

Kafin a gano adadin yawan hakoran sai da likitocin suka yi wa yaron tiyata sannan suka ciro wata jaka da ta kai inci biyar, a ciki ne duk hakoran suke ciki kuma wannan tiyatar ta dauki likitocin kimanin sa’o’i biyar don fitar da abin da ya tattara hakoran a cikin bakin.

Likitocin da ke gwajin cututtuka a asibitin sun kira jakar da ta kunshi tarin hakoran da suna “reminiscent of pearls in an oyster.”

A cewar likitocin sun ce wannan shi ne abu na farko a tarihin duniya da aka taba samun wani dan Adam mai yawan hakora da suka kai wannan adadi a cikin bakinsa.

Shi dai wannan mara lafiyar ya kai shekara hudu yana fama da ciwon ba tare da an gano cutar da ke damunsa ba. Iyayen Rabindran sun taba kai yaron su asibiti, amma ba a binciko cutar ba saboda yaron ya ki bai wa likitocin hadin ka.

Farfesa P Senthilnathan, na asibitin a tsangayar da ake yin tiyatar cututtukan baki, ya ce iyayen wannan yaron sun fara fahimtar akwai alamun cuta a bakinsa tun yana shekara uku saboda dasashinsa yana kumbura. Amma sai suka yi watsi da abin da suka gani ganin cewa kumburin bai yi girma sosai ba, sannan marar lafiya ya ki amincewa da likitocin da za su duba shi hadin kai don gano larurar da take damunsa.

Farfesa P Senthilnathan, ya  ce, da iyayen suka fahimci kumburin yana kara girma ne sai suka kawo shi asibitinsu.

“Mun bude bakin yaro sai ga wani abu kamar jaka a ciki, wadda ta yi nauyin giram 200, a hankali da natsuwa muka fitar da ita, sai ga hakora sun kai 526, cikinsu akwai kanana da matsakaita da kuma manya,” inji Farfesa P Senthilnathan.

Duk da yake wasu hakora kanana ne, amma suna da nau’o’in hakora. Sai mahaifin Rabindran, ya ce na yi zaton cutar kansa ce ta kama dana. Girman wajen da hakoran suke ya kai tsayin santimita 5 yayin da nauyin hakoran sun fi giram 100.

Parbhu, ya ce ban taba tunanin ba cutar kansa ba ce ta kama Rabindran, har sai da likitocin asibitin Sabeetha suka tabbatar min bayan binciken ciwon da aka yi.

Parbhu, ya kara da cewa, a lokacin da Rabindran yake shekara uku na kai shi asibitin gwamnati amma ba a yi masa cikkaken bincike kan abin da ke damunsa tunda daga wannan lokacin ba a kara yin wani magani ba.

“Yanzu haka ina matukar murna saboda dana, ya samu lafiya kuma yana iya cin abinci cikin annashuwa tare da gudanar da rayuwarsa kamar yadda mai cikakken lafiya yake yi,” inji Parbhu.