✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci sun ciro sarkoki da kusoshi masu nauyin kilogiram 1.5 a cikin wata mata

Lokitoci sun yi wa wata mata tiyata, inda suka ciro mata wasu karafuna da suka hada da kusoshi da noti-noti da sarkoki da zobuna da…

Lokitoci sun yi wa wata mata tiyata, inda suka ciro mata wasu karafuna da suka hada da kusoshi da noti-noti da sarkoki da zobuna da abin daure suma, wadanda nauyinsu ya kai kilogiram 1.5.

Matar mai suna Sangita. Likitocin da suka yi wa Sangita tiyatar sun dade su na jinjina irin abin al’ajabin da suka ciro a cikin dan’adam mai rai na mara lafiya wanda take jinya, sakamakon karafen da suka ciro a cikin mara lafiyan.

An dai kai Sangita asibitin Ahmedabad Cibil a kasar Indiya jinya ne lokacin da take fama da matsanancin ciwon ciki.

Likitocin asibitin dai sun ta yi wa Sangita gwajin cututtuka don gano larurar da ke damun Sangita a cikinta, daga bisani suka gano wani tarun abubuwa mai kama da karafa a waje guda.

Mara lafiyan dai ta yi tunanin ta dade tana hadiye karafan na tsawan lokaci wanda hakan yasa karafan suke ta girma a cikinta har ya kai ga cikin ya yi nauyi.

Babban likitan da ke aikin tiyatar Dakta Nitin Parmar na asibitin Ahmedabad Cibil ya ce tumbin Sangita ya koma kamar wani dunkulallen dutse. Bayan hoton tumbin da aka yi da na’urar likita sai hoton ke nuna wani alamar curi abu a waje guda.

Karafunan da ta hadiya yasa ta ya fara yi wa huhunta illa tare wani bangaren cikin tumbin, hakan yasa nan take likitocin suka fara daukan matakan yi ma ta tiyata.

Da aka fara yin tiyatar sai likitocin suka fara ciro abubuwan da ta hadiye mafi yawancinsu karfuna ne masu tsinin. Daya daga cikin abin da aka fara ciro wa shi ne wata sarka da matar aure  mabiya Hindu ke amfani da ita (mangalsutra) don sakawa a jiki a matsayin  al’ada.

Wasu dai sun yi tunanin don haka ta hadiye wadannan karafunan  tun da farko.

Sangita ta dade tana fama da cutar ‘acuphagia’ wanda ke damun mutum idan ya hadiye abin da bai narke wa.

Bayan yi wa Sangita tiyata a asibitin Gwamnati, jama’a da  dama nata mamakin abin al’ajabin da ya faru da ita, sakamakon kwanaki kadan da tayi tana cewa, tana jin ciwo ciki a cikinta.

A yanzu haka dai Sangita zata ci gaba da rayuwa cikin kulawar likitoci don kauce wa daga hadiyar wani abu.