✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Limaman Saudiyya za su ja Sallar Asham a kasashe 35

Ministan Harkokin Addinin Musulunci na Saudiyya Abdullatif Al-Asheikh, ya amince a tura limamai 70 don jagorantar sallolin Tarawih (Asham) da Tahajjud a kasashe 35 na…

Ministan Harkokin Addinin Musulunci na Saudiyya Abdullatif Al-Asheikh, ya amince a tura limamai 70 don jagorantar sallolin Tarawih (Asham) da Tahajjud a kasashe 35 na duniya a lokacin Azumin Ramadan din bana.

Dama ma’aikatar ta saba aika limamai zuwa wasu kasashen lokacin azumi don jagorantar sallolin da kuma wayar wa  Musulmi kai dangane da abin da ya shafi addini.

Gidanr rediyon BBC ya ruwaito Ministan yana cewa hakan wani bangare ne na kokarin masarautar don nuna kulawa da tallafa wa dukkan Musulmi a duk inda suke.

Ya ce limaman za su dora al’ummar Musulmi a kan turba ta gaskiya, su bayyana musu ainihin sakon Musulunci na gaskiya su kuma wayar musu da kai a kan duk abin da ya shafi rayuwar Musulmi.

“An zabi limaman ne daga kwalejojin shari’ah. Dukkansu mahaddata Alkur’ani Mai girma ne kuma masana sosai a addini. Wadannan matasan malamai kwararrun masu wa’azi ne wadanda za su iya yi wa Musulmi bayanin addinin Musulunci sosai,” in ji shi.

Al-Asheikh ya ce masallatai kan cika makil da masu ibada a lokacin azumi don haka babbar dama ce ga limaman su tafiyar da lokacinsu wajen amfanar mutane da wayar musu da kai.

“Limaman za su isar da sakon Musulunci da kuma karfafa danganta a tsakanin Masarautar Saudiyya da kasashen da aka tura malaman,” inji shi

A ranar Litinin ce Ministan ya gana da limaman ya kuma umarce su su zamo wakilai nagari ga kasarsu.

Ma’aikatar ta shirya musu wani taron kara wa juna sani don kara wayar da kansu kan hanyoyin da ya kamata su bi wajen yada sakon Musulunci a kasashen waje.