✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Limamin Bauchi ya nemi a rage kudin aikin Hajji

Babban Limamin Bauci Alhaji Bala Ahmad Limanci ya shawarci gwamnatin tarayya da ta rage kudin aikin Hajji domin a bai wa al’ummar Musulmi damar sauke…

Babban Limamin Bauci Alhaji Bala Ahmad Limanci ya shawarci gwamnatin tarayya da ta rage kudin aikin Hajji domin a bai wa al’ummar Musulmi damar sauke wannan babban farilla da Allah Ya dora a kansu.

Limamin ya yi wannan kira ne a hudubarsa bayan an idar da raka’o’i biyu na sallar Idi a Bauci.

Ya ce ya kyautu gwamnati da shugabanni da su tashi tsaye su kara tausaya wa al’umma ta kuma samo hanyoyin da za a sauwaka musu gudanar da addininsu cikin sauki.

Ya ce “ina kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi la’akari da yawan kudaden ayyukan Hajji da Hukumar aikin Hajji ta kasa ke karba a wajen jama’a ya taimaka a rage wannan kudin domin a saukakawa  alumma.”

Liman Bala ya kuma shawarci al’ummar Jihar Bauchi da su kula da tsaftar muhalli domin samun cikakkiyar lafiya da kuma samun lada a wajen Ubangiji.   Ya ce tsafta tana daga cikin yanki na imani.

Ya kuma yi kira ga alumma da su ba da zakkar fidda kai daga cikin irin abincin da muke nomawasannan ya roki masu kudi su rika taimaka wa marayu da marasa karfi. Sannan ya hori al’umma su guji aikata badala.   Ya ce aikata miyagun laifuffuka abu ne da ke tauye albarka, ya hana ci gaba a cikin al’umma.