Da Dumi Dumi

Littafin Azumi

Babi na Farko: Wajibcin Azumin Ramadan. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta Azumi a kanku kamar yadda aka wajabta ga wadanda ke gabaninku tsammaninku ku yi takawa.” (k:2:183).

364. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Isma’il dan Ja’afar ya ba mu labari daga Abu Suhail daga Babansa daga dalhatu dan Ubaidullahi cewa: “Lallai wani Balaraben kauye ya zo ga Manzon Allah (SAW) kansa duk kura ya ce: “Ya Manzon Allah! Ba ni labarin abin da Allah Ya farlanta mini daga Sallah? Ya ce, “Salloli biyar face in za ka yi nafila,” ya ce, “ba ni labarin abin da Allah Ya farlanta a kaina na Azumi? Ya ce, “Azumin watan Ramadan face in za ka yi nafila,” ya ce, “Ba ni labarin abin da Allah Ya farlanta a kaina na Zakka? Ya ce, “Sai Manzon Allah (SAW) ya ba shi labarin shari’o’in Musulunci, (Bakauyen) ya ce: “Ina rantsuwa da wanda Ya karrama ka ba zan yi nafila ba, kuma ba zan rage komai ba daga abin da Allah Ya farlanta a kaina.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya rabauta idan ya yi gaskiya, ko ya ce, “Ya shiga Aljanna idan ya yi gaskiya.”

365. An karbo daga Musaddad ya ce: “Isma’il ya ba mu labari daga Ayyub daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi azumin Ashura ya yi umarni da yin azuminta. Lokacin da aka farlanta Ramadan sai ya bari (aka bari). Kuma dan Umar ya kasance ba ya azumtarta face idan ya dace da yinin azuminsa.”

366. An karbo daga kutaiba dan Sa’id ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Yazid dan Abu Habib cewa: Lallai Iraku dan Malik ya ba shi labari cewa: Lallai Urwata ya ba shi labari daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: Lallai kuraishawa sun kasance suna yin azumin ranan Ashura a Jahiliyya. Sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya yi umurni da azumtarta har sai da aka farlanta Ramadan. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya so ya azumce ta, wanda ya so ya ci abincinsa.”

ADVERTISEMENT

 Babi na Biyu: Fifikon Azumi
367. An karbo daga Abdulahi dan Maslama ya ce: “Daga Malik daga Abu Zinad daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Azumi garkuwa ne, kada mai yinsa ya sadu da mace, kuma kada ya yi jahilci, idan wani mutum ya nemi fada da shi ko ya zage shi ya ce: Lallai ni, mai azumi ne sau biyu.” Ina rantsuwa da Wanda raina yake hannunSa warin bakin mai azumi ya fi kanshi a wurin Allah Madaukaki daga turaren Miski. Saboda (Allah Ya ce, mai azumi) ya bar abincinsa da abin shansa da sha’awarsa saboda Ni (Allah). Azumi Nawa ne, kuma Ni ne Mai sakawa da shi. Kyakkyawa daya da sakamakon goma misalinsa.”

Babi na Uku: Azumi kaffara ne
368. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: Sufiyan ya ba mu labari ya ce Jami’u ya ba mu labari daga Abu Wa’il daga Huzaifa ya ce: “Umar (Allah Ya yarda da shi), ya ce: Wane ne ya haddace wani Hadisi daga Annabi (SAW) game da fitina? Huzaifa ya ce, “Ni na ji shi yana cewa: “Fitinar mutum cikin iyalansa da dukiyarsa da makwabcinsa da Sallah da Azumi da sadaka suna kankare ta.” Sai (Umar) ya ce, “Ba wannan nake tambaya ba, wanda nake tambaya ita fiinar da take da karfin shiga jama’a kamar taguwar ruwa (kogi). Huzaifa ya ce, “Amma tsakaninka da wancan fitina akwai kofa wanda aka rufe (kulle). (Umar) Ya ce, “Za a bude ne, ko za a karya? Ya ce, “Za a karya ne,” sai (Umar) ya ce, “To wannan da wuya kuma a sake kulluewa (rufewa) har zuwa Ranar kiyama.” Sai muka ce, wa Masruk tambaye shi: Shin Umar ya kasance ya san ko wace kofa ce? Sai ya tambaye shi, ya ce, “Na’am, kamar yadda ya san ban da gobe akwai dare.”

Share