✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Littafin Tarkon Mut’a

Wasan kwaikayo na daya daga cikin hanyoyin rubuce-rubucen fasahar Malam Bahaushe, haka ma rubutacciyar waka. Malam Nasiru G. Ahmad (08065496902) na daya daga cikin mutanen…

Wasan kwaikayo na daya daga cikin hanyoyin rubuce-rubucen fasahar Malam Bahaushe, haka ma rubutacciyar waka. Malam Nasiru G. Ahmad (08065496902) na daya daga cikin mutanen da Allah Ya ba baiwar rubuta waka, don haka bayan ya samu kwafin sabon littafin wasan kwaikwayon da aka wallafa kwanan nan mai suna Tarkon Mut’a, sai ya tsara wadannan baitoci da ya sanya wa taken Littafin Tarkon Mut’a:

 

Taskar Adabi tana lale,

Bisa karo ba na wasa ba.

 

Daren jiya anka ban sako,

Daga Barden Hausa ba wai ba.

 

Ustazu Bashir Malumfashi,

Aikinka ba za mu raina ba.

 

Littafi wanda ka kera,

Tarkon Mut’a abin babba!

 

Bisa wasan kwaikwayo tsarin,

Bai zam gona ta kowa ba.

 

Sai gogaggu na kuttabu,

Dagaji ba za su fara ba.

 

Lale da yawan fasaharka,

Barden burada’u ba rai ba.

 

Littafin za ya amfanar,

Nazarin Adabi ba a bar ba.

 

Godiya nika yi cikin masaki,

Addu’a ba za na daina ba.

 

Allahu Ya dauwamar kauna,

Gare mu Ya kore duk gaba.

 

Idan na biye ina burin,

Nazarinsa ba zan yi sanya ba.

 

Godiya daga Nasiru Ahmad,

Dan uwa da ba zai butulce ba.