✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lokaci ya yi da za a gwada wakilcin mata – Zainab Sulaiman

Zainab Sulaiman Umar matashiyar ’yan siyasa ce da take takarar kujerar majalisar Dokokin daga Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kan. A tattunawarta da Aminiya ta…

Zainab Sulaiman Umar matashiyar ’yan siyasa ce da take takarar kujerar majalisar Dokokin daga Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kan. A tattunawarta da Aminiya ta ce lokaci ya yi da za a zabi mata a madafun iko don a gwada rawar da za su taka wajen ci gaban kasa:

Aminiya: Me ya sa kika shiga siyasa har kike neman mukami lura da kananan shekarunki?

Na fara gwagwarmayar siyasa tun ina karatu a Jami’ar Bayero inda na zama Mataimakiyar Shugaban  Kungiyar Dalibai a shekarar 2015.  Bayan na gama karatu sai na fara harkar kungiyoyin taimakon al’umma har na bude kungiyata da nufin taimakon mata da marayu inda har nake koyar musu da sana’o’i tare da tallafa wa rayuwarsu. Muna wannan hali ne kuma sai na fahimci cewa a harkar siyasa an bar mata da matasa a baya don haka sai na shiga siyasa inda kuma na rika amfani da kungiyata wajen nuna wa mata muhimmancin shiga siyasa.

Ina kuma so in zama misali a wurin ’yan uwana mata cewa muna da damar tsayawa takara kuma a zabe mu. Idan kika dubi tafiyar shugabancin Najeriya babu matasa a ciki. Ya kamata a ce an ba matasa dama a ga abin da za su iya yi. Kullum idan ana magana sai ki ji ana batun wai dadewa a cikin harkar wannan ba shi ne abin dubawa ba. Abin dubawa shi ne wane kudiri dan siyasa ke da shi, ma’ana me zai yi wa al’ummarsa. Wace kuma irin gudunmawa mutum ya ba mazabarsa kafin ya yi tunanin fitowa siyasa. Idan kin duba mafi yawan mata ne ke fitowa kada kuri’a a ranar zabe, amma abin takaici sakamakon rashin wakilci da suke da shi sai ki ga sun tura mota an barin su da hayaki.

Aminiya: A ganinki me yake janyo aka bar mata baya a harkokin siyasa?

A gaskiya kamar yadda na yi magana da mata da yawa suna maganar cewa suna jin tsoron kada su fito takara a karshe kuma a hana su yin takarar ko kuma sai an je ranar zabe a kayar da su. Wannan batu nasu ba wani bakon abu ba ne, domin kamar yadda na lura da gangan ake hana mata yin takara saboda ba a son a ce mace ce ke mulki.

Za ki yarda da ni idan kika dubi Jihar Kano gaba daya duk madafun ikon nan babu mata da aka zaba a tsawon shekara 30 a siyasar da aka taba samun mace a kujerar majalisar wakilai ta kasa. Mu ba mun fito don mu yi fada da maza ba ne, amma abin da muke cewa shi ne cikin kujera 40 da ake da su a Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya kamata a ce an tsoma mata don su wakilci ’yan uwansu mata.

Ya kamata a daina fadin cewa mace ba za ta iya ba, bayan kuma ba a gwada matan an ga iya yinsu ba. Lokaci ya yi da za a ba mata dama don su gwada basirar da Allah Ya ba su. Maza sun shekara 30 suna yi mana wakilci ba tare da samun biyan bukata ba, to me zai hana a jarraba matan a ga nasu irin  salon. Akwai kuma batun rashin kudi wanda mata ba su iya daukar nauyin abubuwa da dama tun daga kan sayen fom zuwa yawon yakin neman zabe da sauran abubuwan da ke bukatar kudi.

Aminiya: Yaya kike ganin karbuwar da kuka samu a wajen jama’a a matsayinku na mata?

Zan iya cewa alhamdulillahi. domin muna bi gida-gida muna neman kuri’unsu, kuma a zahiri muna samun karbuwa kwarai da gaske wajen wayar wa al’umma kai. Wani abin jin dadi shi ne malamai ma sun amince da wannan tafiya tamu tunda dai sun fahimci cewa mu wakilci muka ce za mu yi ba shugabanci ba. Alhamdlillahi mun fito siyasa ce ba wai dole sai mun samu mukami ba, mun san mulki na Allah ne. Idan mun samu falillahil hamdu, idan kuma ba mu samu ba sai mu ci gaba da ayyukan alherin da muke yi wa al’umma domin ba za mu fasa ba don ba don neman takara muka fara ba.

Aminiya: Wane albishir za ki yi wa al’ummar mazabarki idan kika yi nasarar darewa kan wannan kujera?

Zan duba rayuwar mata da matasa da tsofaffi. Ina tunanin in na yi nasara zan yi kokari wajen samar da wata doka ta za ta kula da tsoffafi musamman abin da ya shafi lafiyarsu. Tsofaffin nan fa ba kowa ne ke da dan da zai taimaka masa ba. Za ki ga tsoho ya je a sibiti an rubuta masa magani amma ba ya da kudin da zai saya saboda ba ya da karfin yin sana’a. Kamata ya yi a samar da doka da za ta bai wa duk wani da ya kai shekara 60 zuwa sama damar samun kulawa a fannin lafiya har zuwa samun magani kyauta.