Da Dumi Dumi

Lokutan da suka dace a yi amfani da kayan kwalliya

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan fili namu na kwalliya tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Mata da dama ba su san lokutan da suka kamata su yi amfani da wasu kayn kwalliya ba. Rashin saninsu na haifar da fesowar kuraje a fuska da kuma yamutsawar fuska. Don haka a yau na kawo muku lokutan da suka kamata a yi amfani da hadin kayan kwalliya domin samun ingantacciyar fata mai sulbi da laushi.

  • Don magance kurajen fuska; yana da kyau a samu ‘baking soda’ sai a kwaba shi da kindirmo a rika shafawa a fuska a kullum safe da yamma na tsawon wata daya a sha mamaki.
  • Wanke fuska; yana da kyau a rika wanke fuska safe da yamma a kullum sannan ana shafa masa man fuska a kullum kafin a kwanta barci.
  • Hadin fuska; irin su hadin da ake yi ake shafawa a fuska; kamar su dilke da sauran kayan murza datti a jiki yana da kyau a rika yin su akalla sau daya a mako domin yawan yinsu na illata fata. A maimakon a ga fata na kyau sai a ga tana yamutsewa da feso kuraje.
  • Tausa; yana da kyau a rika yin tausa akalla sau daya a wata domin samun lafiyar jiki da magance kaushi ga wadda ba ta da kaushi akafa sau daya a wata. Amma idan mutum ya kasance mai kaushin kafa ne yana da kyau a rika wankewa sau biyu a rana.
  • Gyaran hammata; za a iya yin wannan akalla sau daya a mako wato hadin gyaran hammata; a samu bawon lemun zaki a busar sannan a daka a tankade bayan haka a zuba ruwan ‘rose’ da kindirmo sannan a kwaba sai a rika shafawa a hammata domin haskaka ta kada ta kasance da duhu.
  • Don haskaka fuska; a samu ruwan ‘aloe bera’ da zuma da kindirmo ko nono da kurkur a kwaba ana shafawa a fuska a kullum kafin a shiga wanka akalla sau biyu a rana.
  • A kasance cikin sanin irin man da ya dace da fuska ba kowane mai za a rika shafawa a jiki ba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya