✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Luwadi da yaro:  Kotu ta tura maigadin makaranta zaman kaso

Babban Kotun Majistare da ke ’Yan Azara a Zariya ta tura wani maigadi mai suna Hamisu Abdullahi wanda akafi sani da ofisa da ke zaune…

Babban Kotun Majistare da ke ’Yan Azara a Zariya ta tura wani maigadi mai suna Hamisu Abdullahi wanda akafi sani da ofisa da ke zaune a bayan Albarka Sinima, a Tudun Wada, Zariya zaman kaso na wata daya kan tuhumarsa da bata luwadi da dalibin makarantar firamare dan shekara bakwai.

Mai gabatar da kara, kuma wakilin Kwamishin ’Yan Sanda, Sufeto Rimbul Napon ne ya gabatar da wanda ake tuhuma a gaban kotun.

Ya ce mahaifin yaron ne ya kai kara ofishin ’yan sanda na Tudun Wada cewa, Hamisu Abdullahi Ofisa mai gadin makaranta ya bata masa da mai shekara bakwai ta hanyar yin luwadi da shi, inda ya ce yaro yana kuka idan ya zo bahaya. Ya ce  matarsa da ke lura da shi ta kula cewa yaron yana cikin wani hali na damuwa idan ana yi masa wanka, bayan ta tambaye shi sai ya shaida mata cewa idan an tashi daga makaranta sai shi Hamisu Abdullahi Ofisa ya kai shi wani lungu a makarantar ya tube masa wando yana sa masa wani abu a dubura bayan ya gama sai ya ba shi bisikit ko Naira biyar har na tsawan lokaci.

Sufeto Rimbul Napon ya ce bayan kammala bincike mai tsawo tare da kai yaron asibiti, sakamakon binciken likitoci ya tabbatar da cewa an lalata yaron kuma hakan ya saba wa sashi na 259 na kundin shari’a na Final Kod.                                                                                                                                                      Bayan karanta wa wanda ake zargin tuhumar da ake yi masa, sai alkalin kotun, Mai shari’a Halima Sani Aminu ta ce kotun ba ta da hurumin yi wa wanda ake zargi hukunci ko ba da belinsa, ta ce za ta tura da shari”at zuwa Ma’aikatar Shari’a don samun shawara.

Don haka ne ta ba da umarnin a kai wanda ake tuhuma gidan yari kafin samun umarni na gaba, sannan aka dage sauraran shari’ar  zuwa ranar 28/8/2019.