✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikaciyar banki ta damfari Sarkin Kano

An gano wata badakala da ta shafi zamba cikin aminci da wata ma’aikaciyar wani banki ta yi, inda ta zare kudi har Naira miliyan 17…

An gano wata badakala da ta shafi zamba cikin aminci da wata ma’aikaciyar wani banki ta yi, inda ta zare kudi har Naira miliyan 17 a cikin tsawon shekaru uku daga wani asusun ajiya na Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji (Dokta) Ado Bayero.
Wannan labarin  ya yi ta yaduwa a hankali a tsakanin jama’a, sai dai kuma dai duk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin makusantan Sarkin Kano, lamarin ya ci tura, saboda abin da kowa yake ganin cewa magana ce mai nauyi.
Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru a daya daga cikin bankunan rukunin farko na kasar nan ne, kuma an bude asusun ajiyar ga Sarkin ne tun a shekarar 1964. Haka kuma binciken ya nuna cewa asusun ya dade ba a amfani da shi, saboda rashin shigarwa ko fitar da kudi da aka dade ba a yi a asusun, sannan kuma yana da kudi a cikinsa da suka kai Naira miliyan 64.
Jami’ar Bankin da ake zargi, mai suna Amina Magaji, wacce kuma aka ce matar wani ma’aikacin wata kafar yada labarai ce, an ce ta samu alaka da asusun ne a matsayin mai kula da shi, sannan kuma ta yi dabarar rubuta takardar neman littafin caki na fitar da kudade a shekarar 2011, da sunan asusun, kuma ta nuna cewa kamar ta samu umarni ne daga mai martaba Sarki.
Daga nan ne ake zargin matar da fitar da kudade a lokuta daban-daban daga asusun, ba da sani ko izinin Sarkin ba, sannan kuma ana zargin tana azurta kanta ne da wadannan kudaden da har suka kai wannan adadin, kafin balli ya tashi.
An gano badakalar ne a yayin da manajan Bankin ya gano sabani a cikin sa-hannun da aka yi amfani da shi wajen fitar da kudaden.
Bayanai sun nuna cewa, maganar ta isa gaban hukumar yaki da almundahanar kudade (EFCC), kuma jami’an hukumar sun damke matar tare da wadansu jami’an bankin su 12, inda suke fuskantar tuhuma a game da al’amarin.