✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata a Jigawa za su fara samun sabon albashi a Disamba

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince za ta biya ma’aikata jihar mafi karancin albashi na Naira dubu 30 daga watan nan na Disamba. Gwamna Badaru ya…

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince za ta biya ma’aikata jihar mafi karancin albashi na Naira dubu 30 daga watan nan na Disamba.

Gwamna Badaru ya fadi haka ne a lokacin da ’ya’yan kungiyar kwadago na jihar suka cim ma matsaya a kan yadda tsarin albashin zai kasance, wanda kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya sanya hannu a madadin Gwamnan jihar, yayin da Shugaban Kungiyar Kwadago Malam Hassan Galadi ya sanya hannu a madadin kungiyar kwadago ta jihar.

Gwamna Badaru ya ce gwamnatin jihar za ta biya Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi daga mataki na 6 zuwa mataki na daya, yayin da daga mataki na bakwai zuwa na karshe za a ba su daga kashi 12 zuwa kashi na 23 a matsayin abin da za a kara musu.

Badaru ya ce batun biyan bashin watanni da suka gabata kuma ba a yi wata magana ba, kuma shi ma Shugaban Kungiyar Kwadago ya ce sun zauna da gwamnatin jihar, kuma sun amince da tsarin karin albashi da za a fara biya daga watan Disamba amma bashin da suke bi na wasu watanni ba a gama yanke shawara ba, amma da zarar sun cin ma matsaya za su sanar da duniya halin da ake ciki.

Sai ya kuma hori ’ya’yan kungiyar da su guji yi wa aiki rikon sakainar kashi, inda ya bukace su da tsaya tsayin daka wajen kula da aikinsu kuma s uguji zuwa aiki a makare.

Ya kara da cewa kungiya ba za ta mara wa duk wani ma’aikacin da ya karya doka baya akan rashin gaskiya.