✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan Kwastam sun kama ’yan fashi da makami

Duk da cewa aikin ma’aikatan Hukumar Kwastam shi ne hana fasakwauri da tattara kudin haraji ga Gwamnatin Tarayya, sai dai wani lamari da ya dauki…

Duk da cewa aikin ma’aikatan Hukumar Kwastam shi ne hana fasakwauri da tattara kudin haraji ga Gwamnatin Tarayya, sai dai wani lamari da ya dauki hankalin al’ummar da ke kan iyakar Seme a Legas, shi ne yadda jami’an hukumar suka yi wa wadansu ’yan fashi da makami kofar rago suka kama su tare da makamansu da kudin da suka yiwo fashi Naira miliyan takwas da rabi.

Babban Jami’in Hukumar Kwastam da ke kula da iyakar Najeriya da kasar Benin  da ke Same, Kwanturola Muhammed Uba Garba ya shaida wa Aminiya cewa jami’ai masu damara, aiki guda suke yi na tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, don haka a wasu lokutan sashe yana yin aikin sashe domin cimma manufar Gwamnatin Tarayya na wanzar da tsaro a kasa baki daya.

“Jami’anmu sun fita aiki ne sai suka samu bayani game da ’yan fashin inda suka yi musu kofar rago suka kama su biyar da kudin da suka yi fashi Naira miliyan takwas da rabi. To ganin wannan ba aikinmu ba ne sai muka mika su ga ’yan sandan da ke yaki da fashi da makami, kuma ina da tabbacin za su rubuta mana su sanar da mu halin da ake ciki idan sun kanmmala bincike,” inji shi.

Ya ce hadin gwiwa da kyakkyawar alaka a tsakanin jami’an tsaron kan iyakar kasar nan ta Seme shi ne ginshikin wanzuwar tsaro a yankin, “Bugu da kari akwai kyakkyawar alaka a tsakanin jami’an tsaronmu na da kasar Benin kasancewar ginin da muke amfani da shi wanda Shugaba Buhari ya kaddamar a kwanakin baya gini ne da aka yi shi a yankin da yake ba mallakin Najeriya ba ne ba kuma na kasar Kwatano ba ne, ginin na Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma ce (ECOWAS). Wannan tarayya a waje guda ya kara mana dankon zumunci ya kuma saukaka zirga-zirga da harkokin kasuwanci a tsakanin Najeriya da kasar Benin,” inji shi.

Kwanturolan ya ce Hukumar Kwastam da ke kula da Shiyyar Seme ta samar da kudin shiga Naira biliyan daya da milyan 260 da dubu 600 a cikin wata biyu da suka shude, kuma hukumar ta kama  shinkafar fasakwauri da man girki da daskararun kaji da kwayar taramol da aka kiyasta kudinsu a kan Naira dubu 918 da tabar wiwi da wanda ke dauke da su wanda kotu ta yanke wa daurin shekara 2  a gidan kaso.

Kwanturola Muhammed Uba Garba ya gargadi masu fasakwauri su nemi sana’a domin hukumar ta Kwastam ba za ta saurara musu ba.