✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’ana da rabe-raben Insha’i da A’antawa

A yau mun kawo rabe-raben Insha’i da A’antawa. Insha’i, gajeren rubutu ne wanda ka iya zamowa labari ko bayani ko wasiƙa ko muhawara. Abin da…

A yau mun kawo rabe-raben Insha’i da A’antawa. Insha’i, gajeren rubutu ne wanda ka iya zamowa labari ko bayani ko wasiƙa ko muhawara. Abin da aka rubuta kuma yana iya zamowa tabbatacce ne wanda ya taɓa faruwa ko ƙirƙirarre. Babban amfanin Insha’i shi ne koya wa yara ’yan makaranta dabarun yin rubutu. Kalmar aAantawa, samammiya ce daga a’a, wacce ke da ma’ana ta kore aiki ko wani abu; abin nufi shi ne cewa, tana nuna rashin samuwa ko faruwar wani abu:

 

Rukunan Insha’i

Abin da ake nufi da rukuni a nan shi ne sashe. Zamowar Insha’i gajeren rubutu bai hana shi samun sassa ba domin ya samu cika. Insha’i yana da rukunai guda uku kamar haka:

1. Gabatarwa.

2. Gundari jawabi.

3. Kammalawa.

Abin so ne Insha’i ya samu waɗannan sassa guda uku, rashin samun ɗaya daga cikinsu ya maishe da wannan Insha’i naƙasasshe.

Gabatarwa

Rukuni ko sashen farko na Insha’i shi ne gabatarwa. A wannan sashe na gabatarwa mai rubuta Insha’i yake yin ɗan taƙaitaccen bayanin da yake ƙunshe da jawabi game da abin da mai rubutun zai yi rubutu a kansa. Ba a son gabatarwa ta wuce sakin layi ɗaya, kuma cikin taƙaitattaun layuka.

Wannan sashe na gabatarwa, sashe ne mai matuƙar muhimmanci a fagen rubutu. Daga gabatarwa mai karatu yana iya kwaɗaituwa da karanta wannan rubutu ko kuma rubutun ya gundure shi ya yi watsi da shi baki ɗaya. Saboda haka abu ne mai kyau, mai rubutu ya tsaya ya rubuta kyakkyawar gabatarwa kuma taƙaitacciya game da abin da yake yin rubutu a kansa.

Gundarin jawabi

Gundarin jawabi shi ne cikakken rubutun da zai bayyana wa mai karatu asalin abin da ake yin rubutun a kansa. A wannan sashe ne mai rubuta Insha’i yake ɗaukar abin da yake yin rubutu a kansa ya yi bayaninsa dalla-dalla, kuma daki-daki a cikin sakin layi daban-daban.

Kammalawa

Taƙaitawa ce ta dukkan abin da aka rubuta tun daga gabatarwa har zuwa sakin layi na ƙarshe na cikin gundarin jawabi. Abin so ne kammalawa ta kasance a cikin sakin layi guda, sannan kuma na ƙarshe wanda daga shi ba wani, kuma mai cin gashin kanta.

Abubuwan lura wajen rubuta Insha’i

Don rubuta nagartaccen Insha’i, abin so ne mai rubutu ya kiyaye waɗannan abubuwa:

1. Kula da ƙa’idojin rubutun Hausa: Abu ne mai kyau a kula da ƙa’idojin rubutun Hausa a lokacin rubuta Insha’i. Wato a riƙa dasa aya a wurin da ya dace, haka ma waƙafi da sauran alamomin rubutu.

2. Sassauƙar Hausa: Amfani da Hausa mai sauƙin karantawa, yana da kyau sosai a fagen rubutu.

3. Yin amfani da gajerun jimloli: Abu ne mai tarin fa’ida ya zamo mai rubutu ya yi amfani da gajerun jimloli a cikin rubutunsa. Tsawaita jimla a wasu lokutan kan rikitar da mai karatu, musamman idan aka yi rashin sa’a ba a ajiye alamomin rubutun da suka dace ba kuma a muhallan da suka dace.

4. Jeranta kalmomi: Jeranta kalmomi a nan na nufin a yi amfani da kalmar da ta dace, kuma a wurin da ya dace.

5. Salo: Amfani da kyakkyawan salon rubutu kan taimaka wajen fito da haƙiƙanin inda tunanin mai rubutu ya dosa. Abin so ne, ya zama an tsara rubutu daki-daki.

Rabe-Raben Insha’i

1. Insha’i na Labari.

2. Insha’i na Muhawara.

3. Insha’i na Bayani.

4. Insha’i na Wasiƙa.

Insha’i na Labari

Shi ne Insha’in da ake bayar da labarin faruwar wani abu a cikinsa. Wato a rubuta wani gajeren rubutu da ke bai wa mai karatu labarin wani abu da ya faru a baya. Wannan labarin kuma na iya zamowa gaskiya ko kuma ƙirƙirarre.

Insha’i na Muhawara

Insha’i na muhawara shi ne Insha’in da ake rubuta muhawara a ciki. Insha’i ne da mai rubuta shi yake faɗin ra’ayinsa dangane da wani abu a cikin rubutun, amma tare da hujjoji. Misali, mai rubutu yana iya cewa noma ya fi kiwo amfani a fannin gona. To, sai kuma ya kawo dalilansa na faɗin wannan a cikin rubutun. Wannan shi ne Insha’in muhawara.

Insha’i na Bayani

Insha’i ne da mai rubuta shi yake yin bayani game da wani abu. Wannan bayani zai iya zamowa siffanta abin ake yi ta yadda da zarar mai karatu ya gama karanta wannan bayani, idan ya ga wannan abu zai iya gane shi, ko kuma bayani yake rubutawa game da yadda ake yin wani abu. Kamar a ce miyar kuka ga misali. Koma dai me aka ɗauka, a cikin Insha’in bayani ana rubuta cikakke, gamsasshen bayani ne game da wani abu.

Insha’i na Wasiƙa

Insha’i ne da mai rubutu ke rubuta labari ko bayani a cikin tsarin wasiƙa.

Ya zuwa wannan gaɓa, mai karatu zai fahimci cewa Insha’i shi ne wani gajeren rubutu wanda ka iya zama labari, muhawara, bayani, ko kuma wasiƙa. Sannan kuma gabatarwa, gundarin jawabi da kammalawa su ke haɗuwa su samar da Insha’i. Idan mai rubutu ya yi amfani da ƙa’idojin rubutu, ya jejjera kalmomin da suka dace a kuma wurin da suka dace, sannan a cikin gajerun jimloli, kuma a cikin sakin layi, sakin layi, kuma ya yi amfani da Hausa mai sauƙi, to, ba makawa zai rubuta Insha’i mai kyau.

A’antawa

Kalmar A’antawa, samammiya ce daga a’a, wacce ke da ma’ana ta kore aiki ko wani abu; abin nufi shi ne cewa, tana nuna rashin samuwa ko faruwar wani abu. Misali: 1.Wancan gida ne.

2. Wancan ba gida ba ne.

Idan muka lura da jimlar farko “Wancan gida ne,” za mu ga cewa ta nuna samuwar gida a wani bigire da ake iya hangowa. Jimla ta biyu kuma “Wancan ba gida ba ne,” ta kore samuwar gidan da ake magana a kansa. Saboda haka wannan jimla ta biyu ta a’antar da jimlar farko.

Ga kuma wani misalin a cikin magana: Ado, kai ne ka zubar da wannan ruwan? “A’a”. Wannan kalma da Ado ya bayar da amsa da ita, ita ake ɗafa wa “ntawa” a goshinta sai ta zama a’antawa duk kuwa da cewa tushen/saiwar kalmar ita ce a, ta zama a’a, sannan aka yi mata ɗafiyar ntawa a goshi ta koma a’antawa.

Ƙa’idojin A’antawa

Ƙa’ida ita ce abar da ke jan ragamar kowane lamari ya tafi yadda ya kamata sannan kuma bai-ɗaya a kowane bigire sannan a kowane lokaci. A’antawa ma ba a bar ta a baya ba.

Kalmomin a’antawa: Ana a’antar da zance da kalmomin ba, kada da marar.

A’antawa da Lokutan Aikatau

Ana amfani da a’antau ba ta sigar ba……ba wajen a’antar da lokutan aikatau masu zuwa:

Shuɗaɗɗen Lokaci: Shi ne aikin da ya wuce. Misali:

• Kura ta wuce.

Ba kura ce ta wuce ba.

• Ka karanta.

Ba ka karanta ba.

• Sun sayar.

Ba su sayar ba.

Lokaci na yanzu: Shi ne aikin da ke faruwa a lokacin da ake magana. A wannan yanayin ana amfani da a’antau ba, sai kuma wakilin suna ya biyo bayanta. Saɓanin yadda muka gani a baya. Misali:

• Suna magana.

Ba sa magana.

• Yana cin abinci.

Ba ya cin abinci.

Sababben Lokaci: Shi ne aikatau ɗin da ke nuna aikin da aka saba yi. Da ba………ba ake a’antar da shi. Misali:

• Kukan zo tare.

Ba kukan zo tare ba.

• Yakan wanke hula.

Ba yakan wanke hula ba.

• Takan kula shi.

Ba takan kula shi ba.

Lokaci na Gaba na I: Shi ne lokaci mai zuwa nan gaba. Ana a’antar da shi da ba………ba. Misali:

• Za su tafi.

Ba za su tafi ba.

• Za mu hau jirgi.

Ba za mu hau jirgi ba.

• Za ka mayar.

Ba za ka mayar ba.

• Za ta dafa tuwo.

Ba za ta dafa tuwo ba.

Lokaci na Gaba na II: Lokaci mai zuwa. Ana a’antar da shi da ba…..ba. Misali:

• Taa rubuta shi.

Ba taa rubuta shi ba.

• Maa nuna masa.

Ba maa nuna masa ba.

Umarni: Ita ce kalmar aikatau da ke nuna umarni. Ana a’antar da ita da a’antau kada. Misali:

• Yi dariya.

Kada ka yi dariya.

• Fice daga nan.

Kada ki fice daga nan.

• Ku tafi.

Kada ku tafi.

Siffa

Ana a’antar da siffofin mai da masu ta hanyar juya su zuwa marar da kuma marasa. Kalmar mai, tana siffanta namiji ko mace mamallaki wani abu guda ɗaya. Jama’unta ita ce masu. Misali:

• Mai mutunci

Marar mutunci.

• Masu mutunci

Marasa mutunci.

• Mai hankali

Marar hankali.

• Masu hankali

Marasa hankali.

Ɗauraya

A’antawa ita ce kore abu. Kalma ce da ta samo asali daga a’a, wacce aka yi wa ɗafiya a goshi da ntawa. Ana amfani da kalmomin ba, kada, marar da marasa wajen a’antar da zance. Ita ba, tana da sigogi guda biyu; ba da take aiki da lokaci na yanzu, sai kuma ba…………ba, wacce take aiki da Shuɗaɗɗen Lokaci, Lokaci na Gaba I da na II, da kuma Sababben Lokaci. Kada, tana a’antar da umarni. Daga ƙarshe kuma, sai marar da marasa da suke a’antar da siffa a jinsin namiji da mace, tilo da jama’u. Marasa, ita ce take ɗaukar jama’u.

 

Mun ciro wannan rubutu daga: Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. Unibersity Press PLC,

Ibadan – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ’Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare 1. Unibersity Press PLC, Ibadan-Nigeria da kuma shafin Intanet.