✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabudan Sha’awar Uwargida (6)

Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo…

Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan yadda wasu cutuka da canzawar yanayin jiki ke iya zama sanadiyyar kullewar sha’awar uwargida da kuma bayani kan mabudi na biyu.   Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

1. Salewar da kumburin labban ’yammatanci:  Shi ma wannan yana haifar da tsananin zafi lokacin ibadar aure, wani lokacin yakan zama ciwo mai tsanani, gwajin likita ne kadai zai tabbatar da irin kwayar cutar da ta haifar da ciwon don magance ta da irin maganin da ya dace. Sannan rashin isashshiya da kuma cikakkiyar tsabtar wajen na daga cikin abubuwan da ke haifar da irin wannan ciwo. Haka nan wasu kayan zamanin da ake amfani da su kamar su sinadarin musamman don wanke ’yammatanci: ‘baginal douche’ da kuma cushe-cushen kayan mata da hakkin maye na iya haifar da wannan ciwo, domin yanayin halittar ‘yammatanci iri daya ne da kwayar idon dan Adam, an halitta su da ruwan da ke wanke su ya fitar da datti ya turo waje, to amfani da ‘baginal douche’ na iya jaza ire-iren wannan matsalolin.

2.  Mannewar yadin cikin kugu guda biyu waje daya shi ma na iya haifar da jin zafin ibadar aure, amma da an yi tiyata an raba su shikenan ciwon zai wuce insha Allah.

3. Haka ma wasu cutuka masu dangane da mahaifa; irin su ciwon kaba na mahaifa; ‘fibroid’ da kaluluwar cikin mahaifa ‘cysts’  duk suna iya sa jin zafi lokacin ibadar aure, hanya mafi dacewa sai a je asibiti don a tabbatar da ainihin abin da ke haifar da hakan, da fatan Allah Ya sa a dace, amin. 

Mabudi  na 2: Matakai Shidan Maigida:

Wannan fili ya samu sakonni da yawa daga magidanta maza, suna tambayar yadda za su yi su bude sha’awar matansu, da masu tambayar me mata ke so a yi masu wajen ibadar aure, da kuma masu son su san yadda za su yi matansu su rika tabuka wani abu cikin gabatarwar ibadar aurensu, da sauran makamantan tambayoyi. Wadannan tambayoyi suna da matukar alfanu kwarai da gaske, alama ce mai nuna su magidantan kwarai ne kuma sun damu da matansu kuma suna tsananin sonsu, saura sai a bi bayanin matakai shidan nan kuma a aikata su a aikace, insha Allah za ku ga matanku sun canza suna maku irin yadda kuke so wajen ibadar aure. 

1. Matakin Farko: Fahimtar Matukan Sha’awar ’Ya Mace:

Wani abun da ke kawo matsala cikin ibadar auren ma’aurata shi ne karancin ilmin yanayin sha’awar juna. Kamar yadda halittar mace da namiji ta bambanta, to haka halayyarsu, hankalinsu da kuma sha’awarsu. Shi namiji Allah SWT Ya inganta ma’aikatar hankalinsa, Ya ba shi karfin basira da aiki da hankali sama da wanda Ya ba ‘ya mace, ita kuma ‘ya mace, Allah Ya inganta ma’aikatar hankalinta da shau’uka masu tsananin karfi da inaganci, sama da na da namiji.

In muka lura da irin yanayin zamantakewar dan Adam, sai mu ga kowannen mu an ba shi abu mafi cancanta da shi a halin zaman rayuwar duniya. Maza su ne masu rike gida da al’umma gaba daya, dole suna bukatar kaifin hankali da basira wajen zartar da ayyukansu. Ita kuma mace, in so da kauna da tausayi ba su cika zuciyarta ba, ya za a yi har ta iya yin hakurin daukar ciki, raino ta kuma yaye  ‘ya’yanta har a samu cikar al’umma?

Yanayin halittarmu yanayin sha’awarmu; da namiji hankali ya fi karfi cikin ma’aikatar hankalinsa, sannan ga kasantuwar sha’awarsa mai tsanantuwa, sai ya kasance biyan bukatar sha’warsa, kodayaushe ita ya sa a gaba, kuma in ya kusanci matarsa, to ba wani abun da zai hana shi cimma biyan bukatarsa, sai dai in akwai wata matsala ta daban. Ita kuwa mace, shau’uka ne suka fi karfi cikin ma’aikatar hanakalinta; kuma kamar yadda muka san rashin tabbas din shau’ukan dan Adam, domin dai ba shaukin da ke tabbata a zuciya kodayaushe, komin karfinsa kuwa, to haka sha’awar ‘ya mace take, ta kan caccanza kodayaushe, ba lallai ba ne abin da ya motso da sha’awa yau ya zama kullum shi zai rika motso da sha’awa. Maigidan da ya fahimci wannan, yana kuma son ya jiyar da matarsa, to sai ya rika sa ido sosai a kan yanayin caccanzawar sha’awarta.

Shau’uka kala biyu ne: Farare da bakake, misali ga kadan daga cikin irin shau’ukan da kan taka rawa cikin sha’anin sha’awar ‘ya mace:

Farare shauki:

Farin ciki

Jin dadi

Natsuwa

Wadatar Zuci

So da kauna 

Bakake:

Yawan  damuwa

Bakin ciki

Jin Haushi

Fargaba

kiyayya

Huzni 

To kafin uwargida ta ji motsuwar sha’awa ta kankama ko’ina a jikinta da ma’aikatar hankalinta, akwai bukatar kasancewar shau’ukan da ke kai kawo cikin zuciyarta a wannan lokacin, ya kasance farare ne suka fi bakaken yawa. A takaice dai matukan sha’awar ‘ya mace guda uku ne: jin dadin zuciya; wasannin ibadar aure da kuma natsuwar rai.  Bayaninsu daya bayan daya na zuwa sati na gaba Insha Allah.

Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.