✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mace-macen Hadejia ba su da nasaba da COVID-19 –Kwamitin bincike

Kwamatin likitoci da gwamnatin Jigawa ta tura Hadejia don binciko musabbabin karuwar mace-macen da aka samu a yankin ya mika rahotansa ga gwamnati, yana mai…

Kwamatin likitoci da gwamnatin Jigawa ta tura Hadejia don binciko musabbabin karuwar mace-macen da aka samu a yankin ya mika rahotansa ga gwamnati, yana mai cewa babu alaka tsakanin rashe-rashen da COVID-19.

Kwamitin ya kuma ce don tantance hakikanin yawan mutanen da suka riga mu gidan gaskiya, ya kidaya sababbin kaburbura 92 a makabartu biyu da ke garin na Hadejia.

Kwamashinan lafiya na jihar ta Jigawa, Dokta Abba Umar Zakari, ya bayyana hakan a Dutse a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mai bai wa gwamna shawara a kan harkokin yada labarai Malam Auwalu Danladi Sankara.

Da yake karin haske a wata sanarwa ta murya da aka wallafa a shafin sada zumunta na Facebook, shugaban kwamatin binciken, Dokta Mahamud Abdulwahab, ya ce a Babban Asibitin Hadejia sun samu bayanan mutuwar mutum 46 a cikin kwana bakwai, yayin da su kuma al’ummar gari suka ba da bayanan mutuwar mutane 44.

Sai dai kuma bai fadi inda aka samo bayanan mutum biyu ba, kasancewar kwamitin ya kidaya kabubura 92.

Maza sun fi yawa

Dokta Abdulwahab ya kara da cewa kamar yadda suka ji daga bakin jama’a a garin na Hadejia, kashi 73 cikin 100 na wadanda suka mutu maza ne.

Kashi 59 cikin 100 kuma, inji shugaban kwamitin, sun mutu ne a gidajensu yayin da kashi 41 suka rasu a asibiti.

Haka kuma, kashi 75 na wadanda suka mutu manyan mutane ne wadanda suka haura shekaru 60 yayin da sauran kashi 15 cikin 100 kuma shekarunsu suka kama daga 40 zuwa 60.

An killace iyalan mutum guda

Ya kara da cewa a binciken da suka yi sun gano galibin wadanda suka rasa ransu a mace-macen na Hadejia da ma suna fama da rashin lafiya kamar hawan jini, ko amosanin jini, ko shanyewar barin jiki, yayin da wasu suka yi fama da ciwon koda wasu kuma ciwon zuciya.

Kuma, a cewar shugaban kwamitin, daga cikin wadanda suka rasu babu wanda ya taba fita daga Hadejia a wata takwas da suka gabata, sannan babu wanda ke dauke da COVID-19 kamar yadda bincikensu ya nuna.

“Mutun daya ne kawai daga cikin wadanda suka mutu, kamar yadda bincikenmu ya nuna, aka ce ya rasu sakamakon zazzabi mai zafi da kuma tari; kuma kafin mutuwarsa yana fama da sarkewar numfashi – tuni shi kuma muka killace iyalinsa”, inji Dokta Abdulwahab.

A farkon makon nan ne dai gwamnatin jihar ta Jigawa ta kafa wannan kwamiti don ya binciko dalilin karuwar mace-mace a garin na Hadejia, bayan da aka ba da rahoton cewa mutum kusan 100 sun kwanta dama a kasa da mako guda.

Shugaban karamar dai ya nuna wa wakilin Aminiya wasu alkaluma da ke nuna cewa mutum kusan 50 ne suka rasu a kwana uku zuwa hudu.